’Yan PDP 4,400 sun sauya sheƙa zuwa APC a Binuwai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mambobin Jam’iyyar adawa ta PDP kimanin 4,450 sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki a Jihar Binuwai.

Masu sauya sheƙar da suka fito ne daga ƙananan hukumomin Katsina-Ala, Ukum, Logo, Kwande da kuma Ushongo sun koma APC ne a ranar Talata.

Gwamnan jihar, Hyacinth Alia, ne ya karɓe su a wani biki a yayin da yake gudanar da rangadin godiya ga al’ummar jihar.

Gwamnan yana yin zagaye a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar ne domin nuna godiyarsa bisa goyon bayan da ya samu har ya lashe zaɓen 2023.

A jawabinsa a wurin karɓar masu sauya sheƙar, Gwamnan Alia ya bayyana godiyarsa kan goyon bayan da ya samu a matsayin sabon shiga siyasa, amma ya kayar da sauran masu neman kujerar.

Daga nan ya jaddada shirinsa na sake mayar da al’ummomin da hare-haren ’yan bindiga suka raba da gidajensu zuwa yankunansu domin ci gaba da harkokinsu yadda suka saba a baya.

Da yake nuna damuwa bisa yadda hare-haren suka addabi yankin Sankera, cibiyar noman doya a jihar, Gwamna Alia ya jaddada cewa aniyarsa ta samar da tsaro a jihar.

Sannan ya ƙara da cewa aikin  ba na gwamnati kaɗai ba ne, dole sai jama’a sun ba da gudummawa domin samun nasara.