‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-14 sun kammala ayyuka a wajen ɗakin gwaji na Wentian

Daga CMG HAUSA

‘Yan sama jannatin ƙasar Sin 3 da suka tashi da kumbon Shenzhou-14, sun kammala ayyuka a wajen ɗakin gwaji na Wentian cikin nasara, kamar dai yadda hukumar lura da ayyukan sama jannati ta ƙasar CMSA ta bayyana a jiya Asabar.

CMSA ta ce ya zuwa ƙarfe 1:35 na jiya bisa agogon birnin Beijing, dan sama jannati Cai Xuzhe ya buɗe ƙofar dakin gwaji na Wentian, kana da misalin ƙarfe 3:33, shi da abokin aikin sa Chen Dong, dukkansu sun fita wajen ɗakin gwajin. Ma’aikatan su biyu, sun koma cikin ɗakin gwajin da misalin ƙarfe 6 saura mintuna 13, bayan kammala ayyuka na tsawon sa’o’i 5, da taimakon ‘yar sama jannati Liu Yang, dake tallafa musu a cikin dakin gwajin.

Ayyukan da ‘yan sama jannatin suka gudanar a wajen ɗakin gwajin, sun hada da kafa na’urorin taimakawa tattaki a wajen kumbon, da sauran wasu kayan laturori da ake buƙata domin gudanar da ayyuka, kana sun tantance ingancin tsarin ayyukan ceto a wajen kumbon.

Bugu da ƙari, jami’an sun sake nazartar tsare tsaren ayyukan sama jannati, da na hannun butumbutumi da aka tanada, da kuma ingancin na’urar killace iska dake cikin ɗakin gwajin na Wentian, da sauran na’urorin dake taimakawa ayyukan tattakin a wajen ɗakin gwajin.

Mai fassara: Saminu Alhassan