Gwamnatin Katsina ta fara bada horo ga ‘yan bijilanti don tunkarar ‘yan bindiga

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta fara horar da ‘yan bijilanti 600 daga cikin mutane 3000 da gwamnatin ta yi alƙawarin ɗauka da kuma ba su horo domin su taimaka wa sauran jami’an tsaron dake jihar wajen yaƙar ‘yan ta’adda.

A madadin Gwamna Masari, mai bai wa gwamnan jihar shawara akan harkar tsaro Ibrahim Katsina ne ya ƙaddamar da shirin fara bada horon a sansanin horar da jami’an Civil Defence dake cikin birnin Katsina jiya Alhamis.

Da yake jawabi Ibrahim Katsina ya bayyana cewa bayar da horon wani mataki ne da gwamnatin ta yanke shawarar ɗauka don inganta tsaron al’ummar jihar.

Ya ce an ɗauko mutanen ne daga dukkan ƙananan hukumomin jihar a yayin da aka fara bai wa ‘yan bijilanti 500 irin wannan horon, yanzu kuma 600 sun shiga, nan gaba kuma za a ƙara jami’ai 1900 da za su samu irin wannan horon.

Ya ci gaba da cewa za a ba su horon tunkarar ‘yan bindiga ba sai sun shigo cikin garuruwa ba, kuma za a ba su horo akan yadda za su tattara bayanan sirri da kuma yadda za su sarrafa bindigogi gami da sauran makamai na zamani.

Shi ma da yake na shi jawabin Kwamandan samar da zaman lafiya da kare afkuwar bala’o’i na hukumar ta Civil Defence ACG Babangida Dutsinma ya sha alwashin bai wa waɗanda za a horarls ɗin horo mai nagarta.

A cewarsa nan bada jimawa ba Jihar Katsina za ta zama jihar da tafi kowace jiha zaman lafiya duba da matakan da gwamnatin ke ɗauka.