Yaushe ƙasashen Yamma za su iya ɗaukar nauyin da ke bisa wuyansu

Daga LUBABATU LEI

Kwanan baya, an gudanar da taron ƙolin ƙasashen Afirka game da daidaita matsalar sauyin yanayi a birnin Rotterdam na ƙasar Netherlands, inda shugabannin ƙasashen Afirka guda shida suka hallara, a yayin da firaministan ƙasar Netherland shi kaɗai ya halarci taron, ba tare da shugabannin sauran ƙasashen Yamma da aka ba su goron gayyata ba, ciki har da Faransa da Norway da Canada da sauransu.

Hakan ya baƙanta ran shugabannin ƙasashen Afirka.

Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall, wanda kuma shi ne shugaban karɓa-karɓa karba na ƙungiyar tarayyar Afirka, ya furta a wajen bikin buɗe taron cewa, “Abin baƙin ciki shi ne, na lura da rashin hallarar shugabannin ƙasashe masu ci gaban masana’antu a wajen taron.

“Na yi zaton idan mun yi ƙoƙari mun bar Afirka har mun zo Rotterdam, to, mutanen ƙasashen Turai da sauransu za su fi samun saukin halartar taron.”

Shugaban jamhuriyar dimokuraɗiyyar Congo, Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, shi ma ya yi suka cewa, “Sanin kowa ne su ne suka fi lalata yanayin duniyarmu.”

Abun hakan yake, kafin ƙasashe masu tasowa suka fara raya masana’antu, tuni masana’antun ƙasashe masu sukuni na yammacin duniya suka fara fitar da iska mai gurɓata muhalli a shekaru kusan 200 da suka wuce.

Dan tasiri kaɗan ne ƙasashen Afirka, da ma sauran ƙasashe masu tasowa suka haifar ga sauyin yanayin duniya, amma illolin da sauyin yanayin ke haddasawa sun fi addabarsu.

A sabo da haka, ƙasashen duniya sun cimma yarjejeniyar sauyin yanayi ta MƊD da ma yarjejeniyar Paris, waɗanda suka bukaci ƙasashe masu ci gaba su ɗauki matakai na ƙayyade iskar Carbon da suke fitarwa, tare kuma da samar da kuɗaɗe da ma fasahohi ga ƙasashe masu tasowa wajen daidaita matsalar.

Sai dai abin takaici shi ne, ba a aiwatar da yarjejeniyoyin yadda ya kamata ba, kuma ƙasashen Turai da Amurka ma sun gaza cika alƙawuran su, na taimakawa ƙasashe masu tasowa wajen tinkarar sauyin yanayi.

Rashin hallarar shugabannin ƙasashen Yamma a wajen taron, ya shaida yadda suke rashin girmama ƙasashen Afirka a kullum, baya ga kuma yadda suke gudun ɗaukar nauyin da ke bisa wuyansu.

Ba kawai sauyin yanayi na shafar makomar ƙasashen Afirka ba ne, har ma yana shafar makomar bai ɗaya ta ‘yan Adam da ta duniyarmu baki ɗaya.

Kamar dai yadda Amina Mohammed, mataimakiyar babban sakataren MƊD ta bayyana a wajen taron, “da fika-fikai biyu ne tsuntsu ke iya tashi”, dole ne ƙasashen Yamma su gane cewa, makomar dan Adam daya ce, kuma su cika alƙawuran da suka ɗauka, tare da ɗaukar nauyin da ke bisa wuyansu, ta fannin daidaita matsalar sauyin yanayi.”

Mai Zane: Mustapha Bulama