Sin da Rasha za su gudanar da taron tattaunawa game da aikin tsaro

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Mao Ning, ta sanar da yau Lahadi cewa, bisa gayyatar da bangaren ƙasar Sin ya yi, babban sakataren majalisar tsaro ta tarayyar Rasha, Patrushev Nikolai, zai ziyarci ƙasar Sin a yau Lahadi da gobe Litinin, don halartar taro na 17 na tattauna batun tsaron Sin da Rasha, gami da taro na 7, na tsarin haɗin gwiwa a ɓangaren aiwatar da doka tsakanin ƙasashen Sin da Rasha.

Mai fassara: Bello Wang