Me ya sa takarar Sheikh Ibrahim Khalil ta zama barazana ga NNPP da APC a Kano?

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Ganin yadda zaɓen gama-gari na 2023 ke ƙara ƙaratowa, Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) kuma ta fitar da ranar fara yaƙin neman zaɓe ga jam’iyyun siyasa 18 da suke da rajista, a yayin da ‘yan takarkaru suka ɗaura ɗamara fita yaƙin neman zaɓen.

Sai dai wannan dalilin ne ake ganin ya sa wata ƙungiya ta manyan masana a harkar aikin gwamnati da sauransu, da ake kira KJPF wato Kano Jigawa Professional Forum, inda ta kirawo ɗaukacin masu yin takara a kowace jam’iyya a Kano domin miqa wani kundi da ta wallafa domin ba ‘yan takara na ɗaukacin jam’iyyu da manufar wannan kundi ya zame ma ‘yan siyasa jagora don ciyar da Kano da Jigawa gaba da zarar sun ɗare kujerun mulki a 2023.

Sheikh Ibrahim Khalil na ɗaya daga cikin masu takarar neman zama gwamnan Kano a 2023 a Jam’iyyarsa ta ADC mai alamar musabaha, da ya halarci wannan taro kamar sauran ‘yan takara na jam’iyyu daban-daban da KJPF ta gayyata wannan taro da aka yi a gidan tunawa da Malam Aminu Kano, wato Mumbaiyya House da ke Unguwar Gwammaja cikin birnin Kano a ranar Lahadin makon jiya.

Bayan haka wani abu da ya ɗaure wa masoyan Malam Ibrahim Khalil kai shi ne duk da bayyana da ya yi a wajen wannan taro, amma an roƙa cire hoton Malamin na bidiyo da mara motsi a kafofin sada zumunta, wanda ƙaƙƙarfar majiya ta tsegunta wa Manhaja, haka kuma majiyar ta yi zargin cewa magoya bayan Jam’iyyar NNPP ne da APC ke wannan cire hoto a lokacin da suke aika shi duniya, wanda ake ganin cewa ba a son ganin hoton malamin a wurin taron kenan?

Wannan al’amari ya sa al’umma musamam masoya ɗan takarar gwamna a Jam’iyyar ADC Sheikh Malam Ibrahim Khalil, kuma Shugaban Majalisar Malamai na Arewa tambaya cewa me ya sa takarar Sheikh Ibrahim Khalil ke barazana ga NNPP da APC? Wato Kwankwasawa da Gandujiyawa?

Haka kuma wata majiya ta tabbatar wa da wakilinmu cewa akwai wani ɗan Jam’iyyar NNPP a Kano wanda ya samu masoya ɗan takarar Jam’iyyar ADC wato Malam Ibrahim Khalil cewa ya janye takararsa wanda daga ƙarshe har wani ofis na kamfe na Jam`iyar ADC ya karɓa ya mai da shi na Jam’iyyarsa ta NNPP maimakon ofis ne na ADC.

Majiyar ta kuma ce ko da gaskiyar hakan ta bayyana sai aka ce a bar masa ofis ɗin Malam dai takararsa na nan daram dam a ADC a 2023 kuma bai janye ba! Ba kuma siyasar tsalle-tsalle yake yi ba.

Har ila yau majiyar ta labarto cewa malamin ya na yawan samun kiraye-kiraye da shawarwari daga wasu jam’iyyun hamayya, na cewa ya haƙura da takarar Gwamna Kano, ya zo ya yi takara Sanata, wanda majiyar ta mu ta ce kullum Malam watsi ya ke da wannan kira, ko wannan shawara daga wasu yan hamayar siyasa a kano da ƙasa baki ɗaya, majiyar ta jaddada cewa Malam na nan, na takar Gwamnan Kano a Jam’iyyar ADC ba kuma mai ba da mulki in ba Allah ba,” inji majiyar Manhaja.

A ƙarshe wakilinmu ya yi iya ƙoƙarinsa na jin ta bakin waɗannan abu ya shafa amma abun ya ci tura daga zarar an ji ta bakinsu zamu kawo muku labarin.