Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan bindiga sun harbe wani babban Kwamandan ‘yan sanda da ke kula da shiyyar Dutsinma, ACP Aminu Umar Dayi, yayin musayar wuta a ƙauyen Yoni da ke Ƙaramar Hukumar Safana a Jihar Katsina.
Rundunar ‘yan sanda, wacce ta tabbatar da harin da aka kai wa tawagar tasu a ranar Talata, ta ce ASP Aminu Umar Dayi da wani jami’insu sun rasa ransu a rangamar.
Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Gambo Isah ya tabbatar wa manema labarai a Katsina, ASP Aminu Umar Dayi ya gamu da ajalisa ne a lokacin da suka je fatattakar ‘yan ta’adda.
Ya ce sun kai ɗaukin gaggawa ne bayan sun samu rahoton ganin tawagar ‘yan bindiga sama 300 a kan mashina ɗauke da muggan makamai a dajin Zakka da ke Ƙaramar Hukumar Safana.
Ko a ranar 18/11/2021 ma, ASP Aminu Umar ya jagoranci irin tawaga suka kai wa jama’ar garin Ɓaure a Ƙaramar Hukumar Safana ɗaukin gaggawa a lokacin da ‘yan bindiga suka kai masu farmaki.
Bayan musayar wuta an kashe ‘yan sanda biyu; ASP Yakubu Joshua da Sajent Zaharadeen Yuguda, yayin da aka kashe ‘yan bindiga biyu, tare da ƙwace bindiga ƙirar AK-47 da harsasai masu yawa.
Kwamishinan’yan sanda na Jihar Katsina Idrisu Dauda, ya bayyana kashe ASP Aminu Umar Daya a matsayin babban rashi a gare su, tare da shan alwashin ci gaba da fatattakar ‘yan bindiga a sassan daban-daban na jihar Katsina.
Jihar Katsina na cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro, ko a makon nan ma sai da ‘yan bindiga suka kai hari a ƙauyen Tamawa a Ƙaramar Hukumar Kurfi, inda suka yi awon gaba da amarya da ‘yan biki, ciki har da matar ma’aikacin gidan rediyon Vision FM da ke Katsina, A’isha Ibrahim Yunusa Dutsinma.
