Sakkwatawa sun fi ɗinkin sallah bana fiye da baya – Shugaban Ƙungiyar Teloli

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Yayin da al’ummar Musulmi ke cigaba da gudanar da shagulgulgulan Babbar Sallah bana ta 1443AH, da alamu a sallar ta zo da yanayi na bazata la’kari da irin yadda al’umma ke ƙoƙarin sabunta suturar da za su gudanar da shagulgulgulan Babbar Sallar bana.

A cewar shugaban Ƙungiyar Teloli na Jihar Sakkwato, Yusuf Muhammad Bello Tafarkin Taloka, sallar bana ga teloli sai sam-barka.

“Alhamdulillah gaskiya yanayin ɗinkin wannan shekarar ya haura na shekarar da ta gabata iya gwargwado kamar yadda kake gani, kamar yadda ake zuwa kara sayen rago haka ake rububin zuwa wajen teloli domin karɓar ɗinki, inji shi.

Yusuf Taloka ya ta’allaka lamarin da yanda Sakkwatawa ke ƙoƙari wajen a duk shekara ta Allah wajen shiryawa bukukuwan Sallah.

Da aka tambaye shi kan yanayin cika alƙawari ga jama’a da wasu lokuta ake samun saɓanin hakan, shugaban ya bayyana cewa ‘wannan ai tsohon zance ne’.

“Wannan a da kenan lokacin da teloli suka yi ƙaranta, Alhamdulillah yanzu lungu da saƙo ana samun teloli  ka ji dalilin raguwar matsalar,” a cewarsa.

Haka ma shugaban ya gode wa gwamnatin Jihar Sakkwato bisa basu damar gudanar da sana’o’insu cikin tsari da doka, da ma ba su kwangilar ɗinka tufafin makaranta ga ɗalibai qarqashin shirin BEZDA.

Ya kuma yi amfani da wannan damar wajen taya al’ummar Musulmi murna kan Babbar Sallar wannan shekara.