Yau APC za ta fara sayar da fom ga ‘yan takara

Daga BASHIR ISAH

An bayyana cewa a wannan Talatar jam’iyyar APC za ta fara sayar da fom na neman tsayawa takara a zaɓuɓɓukan 2023.

Tun farko, APC ta shirya sayar da fom ɗin ne a Asabar da ta gabata amma sai ta ɗage saboda wasu ƙalubalai da ta fuskanta inda aka cim ma matsaya game da sabon lokacin da za a soma sayar da fom ɗin ranar Juma’a da addare.

Sanarwar da ta sami sa hannun babban jami’in yaɗa labarai da ke hedikwatar APC a Abuja, Yusuf Ali, ta nuna ‘yan takarar Majalisar Dokoki a jihohi za su sayi nasu fom ɗin ne a babban ofishin jam’iyya na jiha sakamakon shawarar da jam’iyya ta yanke na tura fom ɗin ya zuwa babban ofishinta a kowace jiha.

Yayin da ‘yan takarar majalisun wakilai da dattawa da gwamnoni da shugaban ƙasa za su sayi nasu fom ɗin a hedikwatar APC da ke Abuja.

Sanarwar ta ƙara da cewa, uwar jam’iyyar APC na la’akari da wa’adin da hukumar zaɓe INEC ta gindaya na kammala sayar da fom ɗin takara ga jami’yyu ya zuwa 3 ga Yuni, hakan ya sa ta ɗauki matakin sayar da takardar takara ta ‘yan majalisar dokoki a babbann ofishin APC na jihohi don samun sauƙin sha’ni.

An kyautata zaton tun a ƙarshen makon da ya gabata uwar jam’iyya ta tura takardun takara na ‘yan majalisun jihohi zuwa ofishinta a jihohi 36 da ake da su domin soma sayar da su ranar Talata.

Nan ba da jimawa ba za a sanar da ‘yan takarar da za su sayi nasu fom ɗin a matakin ƙasa wuraren da za su je su sayi fom ɗin kasancewar ana ci gaba da gudanar da aikin yi wa babban ofishin jam’iyya na Abuja kwaskwarima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *