Zaɓen 2023: Zulum ya bai wa makarantu Borno hutun kwana 8

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Borno ta ba da sanarwar bai wa makarantun jihar hutun kwana takwas albarkacin zaɓe mai zuwa.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin haka ne domin bai wa ɗalibai damar sauke nauyin da ya rataya a kansu lokacin zaɓe.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Ma’aikatar Ilimi ta fitar ta hannun Daraktan hukumar kula da makarantun jihar, Mustapha Bukar Umara, a madadin Kwamishin Ilimi na jihar.

Sanarwar ta nuna hutun zai kankama ne daga ranar Alhamis, 23 ga Fabrairu zuwa Laraba, 1 Maris, 2023, don zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan Majalisar Tarayya.

Sai kuma Alhamis, 9 ga Maris zuwa Laraba, 15 ga Maris, 2023, don zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi.

Ma’aikatar ta aike kwafin wasiƙar sanarwar zuwa ga duka ɓangarori masu ruwa da tsaki a fannin ilimin jihar.

By Editor