Daga WAKILINMU
A karon farko, Jam’iyyar APC ta naɗa kansiloli a cikin Babban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa don zaɓen 2023.
A makon da ya gabata ne Daraktan Ofishi na musamman mai kula da ƙananan hukumomi na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa wa Sanata Bola Tinubu, wato Hon. Kolade Alabi David, ya naɗa Kansilan mazaɓar Gurungawa na Ƙaramar Hukumar Kumbotso da ke Jihar Kano kuma jagoran kansilolin APC na ƙasa, Hon. Muslihu Yusuf Ali, a matsayin Mataimakin Kodineta na Ƙasa (na shiyyar Arewa) don tabbatar da nasarar APC a mazaɓu da rumfunan zaɓe.
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da sakataransa na Ƙungiyar Kansilolin APC, Hon. Kazeem A Abayomi daga Jihar Legas a matsayin Mataimakin Sakataren Gudanarwa.

Takardar naɗin ta nuna cewa; “An yi maka wannan naɗi ne a matsayin girmamawa bisa cancanta, jajijircewa, da biyayya ga jamiyya”
Waɗannan bayanai na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da ta fito ta hannun Yahaya Abdu Yahaya, wanda ya kasance sakataren sashen kansiloli na na ƙaramar hukuma na kwamitin PCC.
