Masarautar Dutse ta yi sabon Sarki

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya amince da naɗin Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse, kuma naɗin ya fara aiki ne take ranar Lahadi.

Naɗin ya biyo bayan amincewar kwamitin zaɓen sarki mai mambobi bakwai na Masarautar Dutse, inda baki ɗaya suka amince da Muhammad Hameem ya zama sabon Sarkin Dutse.

Bayanai sun ce mutum uku ne suka tsaya takarar neman sarautar inda Hameem ya samu nasara.

Majiyarmu ta ce bayan kammala zaɓen, daga bisani aka tura da sunan wanda aka zaɓa ga majalisar sarakunan Jihar Jigawa don amincewarta.

Bayan haka, ita majalisar ta tura sunan Hameem tare da na abokan takararsa ga Gwamnan Jihar, Muhammad Badaru Abubakar, inda ya tabbatar da Hameem a matsayin sabon Sarkin Dutse.

A saƙon fatan alheri da ya aike wa sabon Sarkin, Gwamna Badaru ya taya shi murna tare da fatan Allah Ya yi masa jagora, Ya kuma kare shi a sha’anin jagorancinsa.