Canjin kuɗi ya jefa sojojin da ke yaƙi da Boko Haram cikin yunwa – Ndume

Daga BASHIR ISAH

Sanatan Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa kuma Shugaban Kwamitin Kula da Sojoji na Majalisar Dattawa, Mohammed Ali Ndume, ya ce sauya fasalin Naira da CBN ya yi, ya tsananta cikas wajen yaƙi da Boko Haram/ISWAP da sauran ta’addanci a ƙasa.

Ya ce, matakin sauya fasalin Naira da aka ɗauka ya jefa sojojin da ke yaƙi da Boko Haram/ ISWAP cikin yunwa saboda ba su ga sabbin kuɗaɗen ba balle su samu na sayen kayan abinci a inda suke.

Sanatan ya bayyana hakan ne yayin zantawansu da manema labarai a gidansa da ke Maiduguri ranar Asabar.

Ya ce matsin da CBN ya jefa mutane ya sa saura ƙiris ajali ya cim ma wani soja a lokacin da wasu fusatatu suka yi yunƙarin kashe shi a wajen cire kuɗi a ATM.

Ya ƙara da cewa, baya ga jefa sojoji cikin halin yunwa, haka nan ƙarancin sabbin Naira ya haifar wa sojojin cikas wajen jigilar kayayyakin aiki.

Ya ce duk da dai ba wai yana adawa da matakin na CBN ba ne, amma kamata ya yi a samar da sabbin kuɗin a wadace don amfanin ‘yan ƙasa baki ɗaya.

“Ina sanar da Gwamnatin Tarayya da CBN cewa, matsalar da ake fuskanta ba ta tsaya a kan talakawa kaɗai ba, har sojoji ta shafe su,” in ji shi.