Tsohon Shugaban Ƙasar Pakistan, Pervez Musharraf ya rasu yana da shekara 79

Daga BASHIR ISAH

Marigayin shi ne wanda ya karɓi mulkin ƙasar a juyin mulkin da aka yi a 1999.

Ya rasu ne a Dubai bayan fama da dogon rashin lafiya.

Ya zama Shugaban Ƙasar Pakistan ne daga 2001 zuwa 2008.

A halin rayuwarsa, ya tsallake rijiya da baya a yunƙurin kisa da dama da aka kai masa.

Yana daga cikin waɗanda suka mara wa Amurka baya wajen yaƙi da ta’addanci bayan iftila’in 9/11 duk da adawar cikin gidan da ya fuskanta.

Ya sha kaye a zaɓen da aka gudanar a 2008 wanda hakan ya sa ya bar ƙasar bayan wata shida.