Zaɓen fidda gwani: APC ta ɗage zaɓen ‘yan takarar Shugaban Ƙasa, PDP ta shiga ruɗani

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar APC ta ɗage zaɓen fidda gwanin na ‘yan takarar Shugaban Ƙasa da ta shirya gudanarwa a ranar Litinin, 23 ga Mayun 2022, tare da cewa za ta sanar da sabon lokaci nan gaba.

Duk da dai jam’iyyar ba ta ba da dalilin ɗage zaɓen ba, amma ba wannan ne karon farko da APC ta sauya jadawalin zaɓen fidda gwanin nata ba dangane da shirye-shiryen zaɓen 2023.

Sanarwar da ta nuna ɗage zaɓen ta ce, “An ɗage shirin tantace ‘yan takarar Shugaban Ƙasa da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin,  23 ga Mayun 2022.

“Za a sanar da sabon lokacin da shirin zai gudana nan gaba. Da fatan za a yi haƙuri da dukkan akasin da hakan zai haifar.”

Sai dai wasu na ra’ayin cewa APC ta ɗauki matakin ɗage zaɓen ne don kwashe wa babbar abokiyar hamayyarta PDP ƙafa.

A hannu guda, an samu rikice-rikece a zaɓen fidda gwanin da Jam’iyyar PDP ta gudanar a wasu sassa.

Alal misali, a Jihar Neja zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar Majalisar Wakilai da na Majalisar Dokoki da PDP ta gudanar a jihar bai kammala ba a yankin Ƙaramar Hukumar Gbako sakamkon rikicin da ya ɓalle tsakanin magoya bayan Gimba Tswatagi da na Na Busokun.

Haka dai lamarin yake a Jihar Bayelsa da Jihar Delta da Jihar Osun da Jihar Ogun da sauransu inda aka samu akasi yayin gudanar a zaɓen.