Sabbin gwamnonin Kastina da Neja

An ce sanin gaibu sai Allah. Don haka ban ce jihohin Katsina da Neja dukka an gama zaɓe ba. Amma a fili ta ke jama’a kan bayyana wanda ya yi ficce kuma ake rinjayar da samun nasararsa.

Katsina dai zakara ya kunno kai, tabbas ko mutane dubu mutum guda ne wanda zai zamo ya yi nasara sauran kuma su ɗauki ƙaddara tare da haƙura amma sai idan an kwatamta adalci za a yi zaɓen sauran su amince.

Jihar Neja ga dukkan alamu fitaccen marubucin nan mai kamfanin jaridu na Blueprint wacce ke fitar da jarida Manhaja, Alhaji Muhammad Idris Malagi, dukkanin ’yan takara na jam’iyyarmu APC kun cencenci fitowa nema amma fa a ƙara neman zavin Allah kasancewar ’yan takarar dukkanin su kowa ta tasa a za yi masa, amma dai mutum ɗaya ne zai dace.

Allah kai ma mu zaɓi na ƙwarai, amin amin!

Daga MUKHTAR IBRAHIM SAULAWA a Katsina. 07066434519 – 08080140820.