Daga AISHA ASAS
A duk lokacin da aka tava wani mai muhimmanci da zuciya take so da mutunta shi, zuciya kan girgiza yayin da hankali kan gushe, a daidai lokacin komai zai iya faruwa. Wannan ne yasa duk faɗan da kaga ya ƙazanta to tabata akwai sakin layi a furucin na su.
A ƙasa irin Nijeriya da take da mutane masu mabanbantan ra’ayi da addini, kuma ake so mu zauna lafiya ba tare da wani ya ci zarafin wani ba, to wajibi ne a riƙa sawa baki linzami yayin faɗar magana da ta shafi addini.
Addini a arewacin Nijeriya wani abu ne da yake al’ada ga kaso mafi rinjaye, abu ne da za ka taso a cikinsa, a reneka a ciki, don haka za a iya cewa haƙƙi ne na iyaye ɗora ka akan turban abin da suka yarda da shi a sha’ani na bauta, idan ka yi ma shi riƙon sakainar kasha a lokutan ƙuruciya, to tabbas za a tuhumi iyayenka a lokuta mafi rinjaye. Tasirin addini a zuciyarka yakan samo asali ne daga girman muhalin da ka same shi a cikin gidanku.
Idan kuwa iyaye ne masu tusa addini a zukatan ‘ya’yansu, tabbas su ne masu iya tusa aƙidar tsanar wani ɓangare da ba su yarda da shi ba.
Daga Musulmi har Kirista, dukkansu haifaffun Nijeriya ne, ba ɗaya da zai yi iƙirarin ƙasar tasa ce shi kaɗai, don haka mai ya kamace mu, shine mu koyar da ‘ya’yanmu yadda za su zauna da junansu ba tare da faɗa ba. Ba wai na ce dole sai sun yarda da addinan juna ba, ko sunyi addinin tayani in taya ka ba, kowa ya yi nasa, amma mu san yadda za mu mu’amalanci juna.
A duk lokacin da Musulmi ko Kirista ya dasa ƙiyayar ɗaya ɓangare a zuciyar ‘ya’yansa, to ya kafa wani tubali ne na tashin hankali a gaba. Ba dole sai ta nuna ƙiyayya ga ɗaya ɓangare ne za ka iya tsarkake zuciyar ‘ya’yanka daga sha’awar canza sheƙa daga na ka addinin zuwa kishiyarsa ba. Ka koyar da ‘ya’yanka addininsu kamar yadda kake ciyar da su abinci. Ka ba su ilimin addinin tamkar ruwan sha, sannan ka tabbar ya tarbiyyantu da sanin babu wani addinin gaskiya face na sa tare kuma da gabatar masa da hujjojin da za su tabbatar masa yana kan hanyar gaskiya. Wannan ita ce hanyar da zata kawar da kokwanton da zai iya tasiri har ya koma wani addinin ya bar na ku.
Sai dai a cikin duk wannan aikin, yana da kyau ka yawaita nanata kalmar zaman lafiya tsakaninsa da ɗaya addinin, bai yarda da abin da suke bautawa ba, don haka ba zai yi ibada irin tasa ba, amma ya mutunta nasa zavin kuma yana masa kallo ɗaya saɓanin wanda suke yiwa ɗan’uwansu a addini. Kallon da suke wa ɗan’uwansu a addini shine, kallon ɗan uwan ƙasa da kuma ɗan’uwan addini, yayin da wanda suke da bambancin addini yake da ɗaya, wato ɗan’uwan ƙasa. Idan kuwa hakan ta kasance, ba ta yadda za su dasa wa kansu ƙiyayar da ka iya haifar da fitina a tsakaninsu.
Ban yarda da abin da kake bautawa ba ba yana nufin ban yarda za zama wuri ɗaya da kai mu yi mu’amala ta karatu ko aiki ko kasuwanci ba.
A duk lokaci da muka dasa ƙiyayar wanda ba mabiyi addininmu a zukatan ‘ya’yanmu, to fa za su tafi da shi har girma, a lokacin da suke aiki ko wata mu’amala ta neman duniya, ba zai yiwu a ce duk waɗanda suke kewaye da su su zama mabiya addinin na su ba, don haka za su yi ƙoƙarin bayyanar da ƙiyayyar ga mabiya addinin da ba su yarda da shi ba, to fa a nan ne fitinar za ta fara, kuma babu masaniyar inda zata iya jan birki.