Daga AMINA YUSUF ALI
An yi wa mataimaakin Shugaban ƙasar Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo tiyata cikin nasara. Kuma ana sa ran za a sallame shi nan da kwanaki kaɗan bayan ya ƙara jin ƙwarin jikinsa.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne dai aka yi wa Osinbajo tiyata a cinyarsa wanda tawagar ƙwararrun likitoci suka gudanar a wani asibiti dake yankin Ikejan Jahar Legas.
Mai taimaka wa Mataimakin Shugaban ƙasar a fanni yaɗa labarai, Laolu Akande, shi ya ba da wannan bayani a jawabin manema wanda aka wallafa a ranar Asabar.
A cikin jawabin, Akande ya bayyana cewa, wasu tawagar likitoci sun gudanar da tiyata a kan Osinbajo domin yin aiki a kan wani ciwo da ya addabe shi sakamakon wata karaya da ya tava yi a cinyarsa. Ya ƙara da cewa, amma an kammala aikin cikin nasara.
Akande ya ƙara da cewa, a halin yanzu Matakin Shugaban ƙasar yana cikin koshin lafiya da yanayi mai kyau. Kuma ana sa ran za a sallame shi daga asibiti nan da kwanaki kaɗan.
Wani rahoto da aka samu daga asibitin Duchess International Hospital dake Ikeja a jihar Legas ya bayyana cewa, tabbas su ne suka gudanar da tiyata a kan ƙashin cinyar Farfesa Osinbajo ta dama kuma tabbas aikin an yi shi, kuma an gama cikin nasara.
Har’ila yau, jawabin da asibitin ya wallafa ya bayyana cewa, a halin yanzu Farfesan yana cikin koshin lafiya kuma za a sallamo shi nan ba da daɗewa ba.
