Zanga-zanga: Ya kamata Shugaban Ƙasa ya tashi tsaye, ‘yan Nijeriya na cikin wani hali — NLC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasa, sun shawarci Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya daƙile zanga-zangar da ta kunno kai a faɗin ƙasar ta hanyar tattaunawa da waɗanda su ke shirya ta.

Daily Trust ta rawaito cewa daruruwan ‘yan Nijeriya na gangami domin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar.

Da ya ke tsokaci kan lamarin, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, ya buƙaci shugaban ƙasar da ya gano jagororin zanga-zangar ya tattaunawa da su.

Ajaero ya kuma yi kira ga Tinubu da ya saurari kukan jama’a, inda ya ƙara da cewa miliyoyin ‘yan Nijeriya ba sa jin daɗin halin ƙuncin da ƙasar ke ciki.

Shugaban ƙwadagon ya lura da takaicin cewa matsin tattalin arzikin ƙasar ya sanya iyalai da yawa ba sa iya cin abinci sau ɗaya a rana.

By ukarofi