Ziyarar Buhari a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

A yau ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki a jihar Sakkwato inda ya ƙaddamar da katafaren kamfanin siminti mallakar kamfanin BUA da kuma jajanta wa al’ummar jihar dangane da rasehe-rashen da aka samu a jihar sakamakon matsalar tsaro.

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal tare da muƙarrabansa ne suka tarbi Buhari da tawagarsa bayan da suka sauka a filin jirgin sama.

Sa’ilin da Buhari ya ziyarci Fadar Sarkin Musulmi

Ana sa ran kamfanin Simintin BUA da Shugaba Buhari ya ƙaddamar ya riƙa samar da siminti har ton milyan 3 don amfanin al’umma.

Yayin ziyarar, an ga Shugaba Buhari ya ziyarci fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar tare da rakiyar Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal.

Ana sa ran bayan kammalawa da jihar Sakkwato, Buhari zai faɗaɗa ziyarar tasa zuwa jihar Zamfara don jajanta wa al’ummar kan rashe-rashen da matsalolin tsaro suka haifar a jihar.