Jirgin ‘yan sanda ya yi haɗari a Bauchi

Daga BASHIR ISAH

Wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakar Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, ya yi haɗari a Bauchi bayan da ya baro birnin tarayya, Abuja.

Bayanin aukuwar haɗarin ya fito ne daga Hukumar Binciken Haɗurra (AIB), a ranar Alhamis ɗin nan.

Sanarwar da AIB ta fitar ta ce, “Haɗarin ya auku ne a ranar 26 ga Janairun 2022 da misalin ƙarfe 7:30pm a filin jirgin saman Bauchi.

“Jirgin ‘yan sandan ya baro Abuja ne da misalin ƙarfe 04:54 na rana zuwa Bauchi ɗauke da mutum shida.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, an samu waɗanda suka ji rauni sakamakon haɗarin, amma babu hasarar rai.

Hukumar AIB ta nemi haɗin kan al’umma inda ta ce ƙofarta a buɗe take don karɓar duk wani hoton bidiyo dangane da haɗarin wanda zai taimaka mata wajen aikinta na bincike.

AIB ta ce kada jama’a su yi hasashe kan dalilin aukuwar haɗarin har sai ta fitar da rahotonta a hukumance.