Zulum ya raba wa manoma taraktoci 442 da takin zamani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya raba taraktoci 442 da injinan noma da garmuna guda 312 da kuma takin zamani nau’in MPK ga manoman jihar.


Gwamnan ya bada umarnin bai wa kowacce daga ƙananan hukumomin jihar 27 taraktoci 5, da kuma guda ɗaya ga kowacce daga gundumomi 312 na jihar domin sayar wa manoma a kan rabin farashin da gwamnati ta sayi motocin.

Ya bayyana cewa za a sayar wa manoma taraktocin ne ta hannun ƙungiyoyin haɗin gwiwar manoma.

Da ya ke jawabi yayin ƙaddamar da motocin na noma a Maiduguri, Zulum ya ce, gwamnatinsa ta sayi kayayyakin noman ne domin sayar wa manoma bisa rangwame a faɗin jihar.

Ya kuma bada umarnin kafa kwamitin sayar da kayayyakin noman a kowace ƙaramar hukuma, inda kwamitin zai ƙunshi babban sakataren ma’aikatar noma da albarkatun kasa, babban sakataren hukumar raya ayyukan noma ta jihar, shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a ƙananan hukumomi da kwamitin miƙa mulki na qananan hukumomin da ’yan majalisar dokokin jihar Borno, shugabannin ayyukan gona na ƙananan hukumomin da sauransu a kowace karamar hukumar.

Zulum ya koka kan yadda wasu miyagun da ’yan siyasa suke karkatar da taraktocin da gwamnati ta saya aka raba wa manoma, inda ya ce duk wanda aka samu yana aikata hakan nan gaba za a yi maganinsa yadda, babu sani, babu sabo.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye take ta yi wa kowa hidima ba tare da la’akari da matsayinsa a cikin al’umma ba.

Ya kuma yi alƙawarin ƙara samar da ƙarin kayayyakin aikin noma da takin zamani da irin shuka ga manoma domin rarrabawa a faɗin jihar da zimmar bunƙasa noman rani.

Tun da farko a jawabinsa na maraba, babban sakatare na ma’aikatar noma da albarkatun ƙasa ta jiha Bulama Gana ya yaba wa gwamnan bisa ba da fifiko a fannin noma a jihar ta hanyar samarwa manoman birni da karkara kayayyakin noma da taki, tsaba da tsire-tsire a farashi mai sauƙi.