Ƙasar Sin na adawa da yin shisshigi cikin harkokin gidan ƙasashe masu tasowa bisa hujjar kare haƙƙoƙin ɗan Adam

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Jumma’a cewa, ƙasarsa tana adawa da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan ƙasashen dake tasowa, bisa hujjar kare haƙƙoƙin bil’adama, matakin da kuma ya samu goyon-baya daga sassan ƙasa da ƙasa, musamman ma ƙasashe masu tasowa.

Wang ya yi wannan furucin ne, yayin da yake gabatar da manyan nasarorin da ƙasar Sin ta samu a fannin raya sha’anin kare haƙƙoƙin ɗan Adam. Ya ce tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 18, kwamitin ƙolin jam’iyyar dake ƙarƙashin shugabancin Xi Jinping, yana maida aikin girmamawa, gami da kare haƙƙoƙin ɗan Adam a matsayin wani muhimmin aiki na mulkin ƙasa, don samar da ci gaba ga sha’anin kare haƙƙoƙin ɗan Adam na ƙasar Sin.

Wang ya ƙara da cewa, ƙasarsa na nuna kwazo, wajen halartar ayyukan kare haƙƙoƙin ɗan Adam na duk duniya, kuma har sau uku kwamitin kula da haƙƙoƙin ɗan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da kudirin da ƙasar Sin ta gabatar, dangane da gudummawar da ci gaba ya bayar, ga more dukkanin haƙƙoƙin ɗan Adam, gami da faɗaɗa haɗin-gwiwa a fannin haƙƙoƙin ɗan Adam. Hakan na nufin ra’ayoyin kare haƙƙoƙin ɗan Adam ta hanyar samar da ci gaba, da faɗaɗa haɗin-gwiwa ya shiga zukatan al’ummomin ƙasa da ƙasa.

Wang ya ce, ƙasar Sin tana son yin ƙoƙari tare da ɓangarorin ƙasa da ƙasa, domin samar da ci gaba ga haƙƙoƙin ɗan Adam na duniya, da ƙara ƙirƙiro makoma mai haske.

Mai fassara: Murtala Zhang