Taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar na 20 da muhimmancinsa

Daga LAWAL SALE

A ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba ne aka buɗe taron wakilai karo na 20 na jam’iyyar kwaminis da ke kan karagar mulkin ƙasar Sin (JKS) a Beijing, babban birnin ƙasar Sin, taron dake da muhimmancin gaske, wanda har ya jawo hankalin ƙasa da ƙasa. A wannan karon dai an samu halartar wakilai, gami da waɗanda aka ba su goron gayyata na musamman sama da 2300.

Babban sakataren kwamitin ƙolin JKS, kana shugaban ƙasar ta Sin, Xi Jinping ya bayyana yayin buɗe taron cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu wasu manyan nasarori 3 masu matuƙar muhimmanci, waɗanda suka shiga tarihin JKS da al’ummar ƙasar.

“Mun cika shekaru 100 da kafuwar JKS, gami da mun shiga wani sabon zamani na gurguzu mai sigar ƙasar Sin, kuma mun fatattaki ƙangin talauci baki ɗaya, kana mun kammala ginin al’umma mai matsakaicin ci gaba ta kowanne ɓangare, wato dai, mun cika burinmu na farko a lokacin da muke murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS.”

Haƙiƙa, abin da ya jawo hankalina shi ne, yadda aka fitar da dukkanin mutane da ke fama da ƙangin talauci a karkarar ƙasar Sin da yawansu ya kai kusan miliyan 100, abin jinjinawa ne, wanda kuma ya bayar da babbar gudummawa wajen kawar da talauci a duk fadin duniya.

Ta fannin tattalin arziki kuwa an samu haurawar tattalin arziki ƙaƙƙarfa a shekaru goman da suka wuce. Ma’aunin GDP na ƙasar a ƙarƙashin jagorancin shugaba Xi Jinping a inuwar JKS ya nuna ma’aunin ya karu zuwa kuɗin Sin Yuan triliyan 114 (kimanin dalar Amurka triliyan 17.72), wannan ya ɗauki kaso 18.5 na tattalin arzikin duniya. Ƙasar Sin dai ita ce ƙasa ta biyu mafi girman tattalin arziki a duniya.

A baya baya kuwa yaƙi da cutar COVID-19 ita ma gagarumar nasara ce. Abin jinjinawa ne da burgewa a ganin yadda a ƙarƙashin jagorancin JKS aka yaƙi cutar COVID-19. Gwamantin ƙasar ƙarƙashin shugabancin Xi Jinping ta bayar da duk abin da ya kamata domin ganin an kawar da cutar kamar: kayan gwaje-gwaje da magunguna da gina asibitocin gaggawa da kandagarki a duk faɗin ƙasar. In dai akwai jagoranci na-gari to za’a samu nasara a duk abin da aka yi niyyar aiwatarwa.

Duk wannan ci gaban, da ƙasar Sin take samu ba abin mamaki ba ne, domin kuwa wannan ya samo asali ne daga jagoranci mai inganci da JKS take bayarwa musamman daga shekarar 1949 da aka kafa jamhuriyar jama’ar Sin da kuma daga shekarar 1978 lokacin da aka fara yin kwaskwarima a gida da kuma buɗe ƙofa ga ƙetare, da kuma nasarorin da aka samu a shekaru goman da suka wuce.