Ƙawancen Sin da Afrika na da muhimmanci ga cimma ajandun nahiyar da na duniya

Daga CMG HAUSA

Masana sun bayyana muhimmiyar dangantakar dake tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afrika, a matsayin mai matuƙar muhimmancin da za ta taimakawa nahiyar aiwatar da ajandunta da ma na duniya, ta hanyar ba matasanta horon fasahohi.

Masanan sun bayyana haka ne yayin wani taro mai taken “Makomar haɗin gwiwar Sin da Afrika: taron shugabannin matasa”, wanda ya gudana a ranar Alhamis a Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Da take jawabi, ministar kula da harkokin mata da walwalar al’ummar ta Habasha, Ergogie Tesfaye, ta ce taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC da aka ƙaddamar a shekarar 2000, kyakkyawar dabara ce ta warware matsalar karancin fasahohi da ƙasashen Afrika ke fuskanta.

A cewarta, haɗin gwiwar Sin da Afrika da hulɗarsu ta diflomasiyya na faɗaɗa a ɓangarorin tattalin arziki da zaman takewa da siyasa, tana mai cewa, ɓangarorin biyu sun kasance masu toshe duk wani kutse daga wurare daban-daban na duniya.

Bugu da ƙari, ta ce aiwatar da ajandun nahiyar da na duniya, kamar ajandar AU ta shekarar 2063 da ta muradun ci gaba masu ɗorewa ta shekarar 2030, sun dogaro ne ga ƙarfin fasahohi da ilimin matasa, don haka, muhimmin haɗin gwiwa dake tsakanin Sin da Afrika na tattare da ɗimbin moriya.

Mai fassara: Fa’iza