Wang Yi ya gana da jakadan Amurka da ke Ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA

Ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi ya gana da jakadan ƙasar Amurka da ke ƙasar Sin, Nicholas Burns, a jiya Jumma’a.

Wang Yi, ya yi maraba da Nicholas Burns a matsayin sabon jakadan ƙasar Amurka a ƙasar Sin, kana ya bayyana cewa, yanzu an shiga lokaci mai muhimmanci na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Kuma ƙasa da ƙasa suna fatan ganin an raya dangantakar ta su yadda ya kamata.

Ya kara da cewa, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ya kamata Sin da Amurka su girmama juna, da yin zama tare cikin lumana, da yin haɗin gwiwa da samun moriyar juna, wanda shi ne tushen raya dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu.

Haka kuma, a matsayinsu na manyan ƙasashe a duniya, Sin da Amurka ba za su iya sauya tsarin juna ba, don haka bai kamata ƙasar Amurka ta yi amfani da matsayinta na ƙasa mafi ƙarfi yayin da take mu’amala da Sin ba, kana kada a yi yunƙurin hana ci gaban ƙasar Sin.

Bugu da ƙari, Wang Yi yana fatan jakadan, zai zama gada wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.

A nasa ɓangare, Nicholas Burns ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin tana da muhimmanci sosai ga ƙasashen biyu, har ma ga duk duniya baki ɗaya.

Kuma ƙasar Amurka tana son ƙara yin mu’amala da ƙasar Sin, da daidaita matsalolinsu, da kuma sa kaimi ga haɗin gwiwarsu.

Mai fassara: Zainab