Aikin gona da kayayyakin tarihi na jawo kankalin Shugaban Ƙasar Sin sosai

Daga CMG HAUSA

A Alhamis ta makon jiya, yayin da aka shiga lokacin girbin tuffa a ƙauyen Nangou na birnin Yan’an dake lardin Shaanxi na Arewa maso yammacin Sin, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya yawata a cikin gonar tuffa domin fahimtar yadda aikin girbi na bana ke gudana.

Yayin rangadin, Shugaba Xi ya gano yadda fasahar ban ruwa da na tantance ’ya’yan itatuwa a ƙauyen Nangou ke ci gaba da samun tagomashi, inda ya yaba da yadda aka raya sana’ar shuka tuffa, wadda ta kasance a sahun gaba, kuma mai kyakkyawar makoma.

Har ila yau, Xi ya jaddada cewa, wajibi ne a inganta farfaɗo da yankunan karkara da aiki tuƙuru domin cimma zamanantar da ayyukan gona da yankunan karkara.

Sannan a jiya Juma’a, shugaba Xi Jinping ya kai ziyara wurin adana kayayyakin tarihi na Yinxu dake zaune a arewa maso yammacin birnin Nanyang na lardin Henan dake tsakiyar ƙasar Sin, kuma fadin wurin ya kai murabba’in kilomita 30, kuma shi ne wurin adana kayan tarihi na wannan tsohon birnin Sin, wanda ya kasance wurin da aka fi gudanar da bincike kansa, kuma mafi faɗi a ƙasar Sin.

A yayin da yake rangadi a wurin, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, al’adun gargajiya na ƙasar Sin tushe ne na sabon tunanin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin, kuma ya kamata a yada managartattun al’adu, da ƙara alfahari da ƙasar Sin.

Bugu da ƙari, a safiyar Juma’a, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya ziyarci wata magudanar ruwan dake gundumar Linzhou dake arewacin lardin Henan na ƙasar Sin.

Wannan magudanar ruwa ta ratsa ta tsaunin Taihang, ana kuma kiranta “magudanar ruwa ta Red Flag”, ta kasance aikin samar da ruwa da aka haka a cikin babban tsaunin Taihang a shekarun 1960 domin warware matsalar ƙarancin ruwan sha da ta shafi mutane sama da 500,000.

A yayin da yake duba yadda wannan magudanar ruwa take aiki yanzu , Xi Jinping ya ce tsarin gurguzu aiki ne da har yanzu ake yinsa, bai tsaya a da can baya kaɗai ba, yana mai cewa, zai ci gaba har a sabon zamani.

Mai Fassara: Fa’iza Mustapha, Zainab Zhang