Dakatar da yajin aikin ASUU

A kwanakin baya ne Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni 8 tana yi, wanda ta fara a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022.

ASUU ta bayyana cewa ta janye yajin aikin ne biyo bayan shiga tsakani da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, da sauran ’yan Nijeriya masu kishi ƙasa suka yi da kuma umarnin kotun ɗaukaka ƙara na neman mambobinta da su koma bakin aiki.

Kotun ɗaukaka ƙara ta amince da hukuncin da ƙaramar kotun ta bayar tare da umurtar ƙungiyar ASUU da ta bi hukuncin da ƙaramar kotun ta yanke a matsayin sharaɗi na sauraron ƙarar. A bisa bin umarnin, ASUU ta dakatar da yajin aikin.

Tare da dakatar da yajin aikin, ana sa ran cewa ayyukan ilimi za su koma gadan-gadan a jami’o’in gwamnati nan ba da jimawa ba. Duk da haka, akwai muhimman batutuwan da ya kamata a magance su sosai don kaucewa wani yajin aikin a cikin jami’o’in gwamnati a nan gaba.

A cewar shugaban ƙungiyar ta ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, har yanzu ba a kai ga shawo kan matsalolin da suka sa aka ɗauki tsawon watanni takwas ana gudanar da yajin aikin ba. Ina neman waɗannan kuɗaɗe ne don farfaɗo da jami’o’in gwamnati da sauran buƙatun malamai.

Ƙungiyar ta ce tsarin IPPIS da gwamnati ke amfani da shi wajen biyan dukkan albashin ma’aikatan gwamnati, kuma ta yi niyya har zuwa manyan makarantun gaba da sakandare, yaudara ce kuma ba ta san irin abubuwan da jami’o’in ke da su ba. Ƙungiyar ASUU na kuma neman a sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009 da ta shiga da gwamnati.

Tun da farko dai gwamnatin ta yi wasu alƙawurra na magance buqatun malaman jami’o’in. Don haka, muna kira gare su da su warware duk wasu batutuwan da ba su dace ba ta hanyar warware taƙaddamar.

Tunda batun kuɗaɗe ne tushen rikicin, ya kamata ASUU da gwamnati su yi amfani da damar da kotun ɗaukaka ƙara ta ba su don ganin an warware matsalar.

Ba za a iya sasanta batun tsakanin gwamnati da ASUU ta hanyar kotu ba. Ya kamata duk masu ruwa da tsaki su tattauna tare da tabbatar da cewa kalandar ilimi ta daina rushewa.

Dole ne malaman jami’o’i su fito da hanyoyin da ba za su wargaje tsarin ilimi ba don magance duk wata taƙaddama da gwamnati. Babu shakka, yajin aikin ya yi illa ga tsarin ilimi na ɗalibai a jami’o’in gwamnati na qasar. Hakanan ba shi da kyau ga malamai da sauran ma’aikata a cikin tsarin jami’a.

Tsakanin yajin aikin na 2020 da yajin aikin na baya-bayan nan, an kusan rasa wargaza tsarin ilimi. Ɗalibai da yawa kuma sun yi watsi da shirye-shiryensu na ilimi. Rushewar kalandar ilimi ta shafi ingancin koyarwa da koyo. Bai kamata a ƙara barin irin wannan yajin aikin ba saboda munanan tasirinsa ga ilimin ɗalibai.

Abin farin ciki shi ne, gwamnati ta ware kimanin naira biliyan 300 a kasafin kuzin baɗi domin farfaɗo da jami’o’in. Ya kamata ’yan Nijeriya su matsa wa gwamnati lamba kan ta saki kuɗaɗen ga jami’o’i a cikin rubu’in farkon shekara. Ya kamata a saki asusun da wuri don haifar da tasirin da ake so. Idan kowace jami’a ta samu Naira biliyan 2 zuwa ko 3, hakan zai taimaka matuƙa wajen inganta al’amura a cibiyoyin ilimi.

A nata ɓangaren, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta nuna kulawa kan batutuwan da ƙungiyar ASUU ta gabatar, musamman wajen ba da fifiko kan ilimin jami’a. Duk ƙasar da ba ta sanya ilimi a gaba ba, tana wasa ne kawai da makomarta.

Bai kamata gwamnati ta kalli umarnin kotun ɗaukaka ƙara da qungiyar ASUU ta bayar a matsayin wata dama ta warware matsalar a cikin yanayi na samun nasara ba. Ya kamata gwamnati ta kuma yi tunanin wasu hanyoyin samar da kuɗaɗe ga jami’o’in gwamnati, gami da ba su cikakken ‘yancin cin gashin kansu ta yadda za su iya karɓar kuɗaɗen da suka dace don ayyukansu.

Muna yaba wa Shugaban Majalisar Wakilai da sauran ’yan Nojeriya masu kishin ƙasa bisa yadda suka shiga tsakani wajen ganin an nufe wannan babi mai ban tausayi a ɓangaren ilimin manyan makarantun ƙasar nan.

Fiye da komai, gwamnati ta gaggauta ɗaukar matakin biyan malaman albashin da suke bi a cikin watanni takwas da suka gabata. Yin hakan zai sa malamai su koma aji da wuri. Hakan kuma zai zama matakin farko na warware matsalar.