Dauda Kahutu Rarara cin mutuncin ya isa haka ko kuwa?

A wani lokaci ɗan na yi rubutu rangaɗeɗe a kan mawaƙin zamani Dauda Kahutu Rarara ɗan mutanen Katsina bisa ga niyya kyakkyawa. Ban sanshi ba, ban taɓa ganinsa ba, illa kawai ƙauna ta mutum da mutum. Dauda Kahutu Rarara bakatsine ne, kuma wataƙil mazaunin Kano wanda ga almajiranci Allah Ya hore masa hikimar waƙa! Ban san ta yadda wannan fasaha ta samu ba, wanda cikin ƙanƙanin lokaci Dauda Kahutu Rarara wai har kyautar mota yakeyi da miliyoyin Naira!

Dauda Kahutu Rarara ance yana kusa-kusa da Villa har ma wai ya kusanci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, a kasancewarsa mawaƙin Shugaba Buhari da kuma cewa ya fito ne daga jihar Katsina, jihar Katsina itace jihar Shugaba Buhari, kuma shi wannan sabon mawaki wai sunan ƙauyensu Kahutu, wataƙila vangaren Daura yake ko kuma can hanyar Ɗandume Allah masani.

To Dauda Kahutu Rarara ya canza kalar waƙarsa ta kasance ta cin mutuncin masu shi, abin mamaki kare da tallan tsire; Dauda Kahutu Rarara ya taɓa mutuncin wasu manyan ‘yan siyasar Kano; wato Maigirma Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau, tsohon Gwamnan Kano kuma mai muƙamin sarauta a Kano kuma yanzu Sanata a tarayyar Nijeriya. Yasa masa suna Duna, wato kare kenan ko? Haka ya kira tsohon Gwamna, kuma tsohon Sanata Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso Tsula wato Biri, haka yanzu kuma yake kiran Gwamna Ganduje da sunan Hankaka!

To duk wannan ga alamu, ya gane cewa ‘yan siyasar Kano basa mutunta junansu har wani can daga jihar Katsina zaizo da ƙoƙon bara yake ciwa manyan Kano mutunci saboda rashin ta ido, domin Wallahi Tallahi Dauda Kahutu Rarara bana jin koda sau ɗaya zai yiwa masari Gwamnan Katsina wannan cin kashin haka, kai bama Gwamna Masari ba, ko ɗan jagaliyar siyasar Katsina idan akwai Dauda Kahutu Rarara bai isa yayi masa cin fuskar da yake yi wa shugabanni a Kano ba.

Gaskiya dama ance Allah wadan naka ya lalace; domin kowa yasan lalacewar siyasa a Kano don haka aka cuso wani yaro “stooge” wasi shi Sha’aban Ibrahim Sharaɗa daga wai Villa aka roƙi Gwamna Ganduje ya sama masa wuri a Municipal don ya zama wakilin majalisar tarayya: Ashe- Ashe an yi haka ne domin tozarta Gwamna Ganduje daga Villa!

Wannan kawai kekecine, ƙila-wa-ƙala amma yaron irin tutsun da yake yiwa gwamnatin jihar Kano da tsiwar da yake yi tabbas akwai iyayen gidansa wanda a ɓoye suke nuna ƙiyayya ga Gwamna Ganduje. Yaron nan yana faɗin abubuwa na gaɓunta kuma yana kashe kuɗaɗe fiye da kima saboda ya samo ɗaurin gindi sosai wanda yanzu Gwamnan Kano aka turo shi ya yi!

To wannan alamu ta yadda wannan yaro Sha’aban yake rangwaɗa kasan akwai walakin; yanzu haka ya tsinto wasu wai ‘yan baka suna taya shi cin mutuncin mutane a radiyo, cikinsu shine har da Dauda Kahutu Rarara, mawaƙin shugaba Buhari, shugaban ƙasar Nijeriya, shaguve da kake yiwa Ganduje cewa Hankaka, kanayi wannan abu amma gaskiya da wanda kakeyi don shi shine dangin Hankaka:

Dauda Kahutu Rarara duk sunan da zaka yi, komi daɗewarka a duniya, ba zaka kai shata ba, wato Mammalo Shata na Bilki sai dubu ta taru Allah Ya jiƙansa amin. Saboda haka juyawa Ganduje baya abune kamar kayi kuma ka gama: Habaici da cin mutunci baya ƙarko ga mai yinsu, wani mawaƙi yace baya tsoron Allah fiye da wani Sarki, kaga sai buzunsa, to ashe akwai lokacin dashewarsa. Ayi a hankali Dauda Kahutu Rarara, yaro bari murna karensa ya kama zaki.

Comrade Ibrahim Abdu Zango, Chairman: Kano Unity Forum, Kano, Nijeriya, 08175472298.