Ƙungiyar Bayar da Tallafi ga Marayu tana iyakar ƙoƙarinta a Legas – Abdulgiyasu Rano

Daga BALA KUKKURU a Legas

Babban shugaba mai kulawa da samar da cigaban kasuwancin ɓangaran tumatiri a kasuwar mile12 da ke cikin birnin Legas, kuma babban uba ga Ƙungiyar Bayar da Tallafi ga Marayu a Kasuwar ta Mile12, Alhaji Abdulgiyasu Sani Rano, ya bayyana irin ƙoƙarin da ƙungiyar ta bayar da tallafa wa ga marayu a unguwar mile12 da kewayanta dama Jihar Legas gaba ɗaya.

Abdulgiyasu, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya. ke zantawa da Jaridar manhaja a Legas a game da al’amuran da suka shafi ayyukan ƙungiyar ta marayu a Legas.

Ya ce, haƙiƙa ƙungiyar tana yin ƙoƙari a game da gudanar da ayyukanta na kulawa da al’amuran da suka shafi marayu a Legas inda a cewarsa ko akwanakin bayan daf da babbar salla ƙungiyar ta tallafa wa waɗansu yara marayu da maƙudan kuɗaɗe masu yawa domin su yi ɗinkin.

Ya ce, kuma ta sayi kayan abincin salla da yawan yaran marayu waɗanda suka amfana da wannan tallafi adadinsu ya kai sama da yaro dubu ɗaya.

Ya ƙara da cewa, akan hakan nema ya ke ƙara yin kira da babbar murya ga al’ummar musulmi mazauna cikin garin Legas dama na ƙasar nan baki ɗaya da sauran masu hannu da shuni injishi musamman musulmi da suke ra’ayin gabatar da tallafin su na yara marayu a wannan ƙungiya da su ƙara ƙoƙari wajen sanya hannuwansu guda biyu a bisa kan wannan al’amari.

Ya ce, da fatan Allah ya shigema kowa gaba a bisa kan ayyukansa na alheri da ya ke cigaba da yin tsokaci a bisa kan cigaba da ya ke ganin kasuwar ta mile12 tana qara samu a kowanne lokaci.

Alhaji shehu usman samfam an samu haɗin kawunan shuwagabannin ɓangarorin kasuwar da iyayanta da ’yan in kiya masu sauke kayan miya da kayan abinci kowanne iri da sauran ‘yan kasuwa masu gudanar da harkokin kasuwancin a cikin kasuwar ta mile12 baki ɗaya.