Gwamnatin Bauchi za ta biya garatuti ga tsoffin ma’aikata fiye da Naira biliyan 20

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya ji takaicin yadda ma’aikacin gwamnati zai kwashe shekaru 35 yana gudanar da aikin hukuma, kuma bayan ya gama wa’adinsa na aiki a ce biyan haƙƙinsa ya kasance wani jidali.

Sanata Bala Mohammed ya lura da cewar, gwamnatoci da suka shuɗe a Jihar Bauchi sun yi sakaci sosai wajen biyan haƙƙoƙin ma’aikata waɗanda suka kammala wa’adin aiki na shekaru 35, yana mai bayyana cewa wannan hali na rashin tausayi da gwamnatocin baya suka nuna wa tsoffin ma’aikata shi ne ya haddasa taruwar kuɗaɗen garatuti akan gwamnatin jiha.

“Ma’aikata suna shan wahala, kuma shekaru aru-aru ba a biyan garatuti. Ba mune muka zo muka qi biya ba, mun zo mun gaji ɗimbin bashin garatuti da ake bin gwamnatin jiha, saboda haka dole mu yi amfani da ilimi, hikima, basira, da dukkan abubuwan da sauran gwamnatoci suke yi a wajibi domin bayar wa ma’aikata haƙƙoƙinsu.”

Gwamnan, wanda yake jawabi a yayin da yake rattaɓa hannu akan wasu dokoki guda goma sha biyu, cikinsu har da dokar kafa hukumar tara kuɗaɗen garatuti daga ma’aikata da suke bakin aiki, ya bayar da tabbacin cigaba da biyan kuɗaɗen fansho wa tsoffin ma’aikata na wata-wata da gwamnatinsa take yi babu fashi.

Ya kuma bayyana cewar, gwamnatinsa tana kan shige da fice ta hanyoyin da suka dace domin ganin an bai wa tsoffin ma’aikata haƙƙinsu na barin aiki, wato garatuti waɗanda gwamnatocin baya suka jibge ba tare da biya ba, haɗi da waɗanda suka hauhawa a wannan lokaci na gwamnatin PDP mai jan ragamar jiha.

“Tun magabatan gwamnatoci na jihar Bauchi da suka shuɗe aka yi wasa da biyan kuɗaɗen garatuti, abinda ya sanya waɗannan haƙƙoƙi na tsofaffin ma’aikata suka taru suka yi yawa, shi ya sa dole sai mun yi wani hovvasa, mun samu wata hanya mai ƙarfi wacce za ta kai mu ga nasarar share dukkan basussukan garatutin ‘yan fansho ɗungurungum.”

Ya ce: “Kuma maganar bayar da gudummawa a cikin fansho, dama tun fil’azal fansho ana ɗaukar wani kuɗi na ma’aikaci, shi ya sa ake biyan fansho ɗin, to amma ba a iya ajiye shi a wani asusu wanda zai kasance mai amfani, sai a dinga kashewa.

“Wannan hali shi ya haddasa gazawar biyan kuɗaɗen fansho da garatuti a wasu jihohi,” inji gwamnan.

Ya ƙara da cewar, akwai ɗimbin kuɗaɗe a hukumar PENCOM, kuma jihohin da suka kafa makamancin wannan doka ta hukumar hidimomin fansho da garatuti wanda gwamnan yake sanyawa hannu, ana iya ba su dukkan yawan kuɗaɗen da suke buƙata bashi na iya wa’adin yawan shekaru.

Jaridar Manhaja ta jiyo daga wani tushe mai ƙarfi na cewar, gwamnatin jihar Bauchi tana gab da kammala shawarwari da hukumar PENCOM ta ƙasa inda tattaunawar za ta kai ga Bauchi ta samu rancen zunzurutun kuɗaɗe kimanin Naira biliyan talatin domin warware dukkan wasu basussukan tsofaffin ma’aikata na jiha.

Dangane kuma da dokar kafa hukumar kula da safara a cikin birnin Bauchi da kewayenta kuwa, wato BAROTA, sai gwamnan ya ce gwamnatinsu ta PDP tana lura da yanayin zamantakewar jama’a, haɗi da lura da tattalin arziki.

Ya bayyana cewar, dalilin da ya sanya a can baya aka hana sana’ar Acava, shine saboda cutar sarƙewar numfashi, wato Korona wanda a lokacin da cutar take qamari, ba a son mutane biyu su hau kan babur guda suna sarƙafa numfashinsu a lokaci guda, domin gudun yaɗuwar cutar.

“Yanzu ga dukkan alamu cutar ta Korona ta kau, kuma ba a kawo wata sabuwar hanya da jama’a za su gudanar da lamuran sufuri ba, don haka ba daidai mu hana yin sana’ar Acava. Mun yi magana da jami’an tsaro, cin rashawa da ma’aikata suke yi kan sana’ar Acava, ba gwamnati ce take sa suba, zalunci ne, kuma muna ƙoƙarin hanawa.

Gwamna Bala Mohammed sai ya bayyana cewar, “ga shi a yanzu Gwamnatin Tarayya tana ƙoƙarin hana aiki da hawa babura saboda yanayin gurɓacewar tsaro. Ana amfani da babura ɗari biyu, ɗari uku ana farmaki wa jama’a, masana’antu ko hukumomin gwamnati, ana karkashe jama’a babu gaira babu dalili.

“Amma, ‘yan acava mutane ne, su hanyar cin abincin sune, kuma sana’a ce, kuma jaura ce, bai kamata a ce an hana su gudanar da wannan sana’a ba saboda wani dalili na son kai ba, amma abubuwa da ake yi masu a gaskiya bada hannun gwamnatin jihar Bauchi ba ne”, inji Ƙauran Bauchi.

Gwamnan ya ce dangane da haka ne, gwamnatinsa ta bijiro da wata hukumar tsaro wacce za ta ƙunshi ƙungiyoyin bijilanti, kwamitocin unguwanni-unguwanni na tsaro, da dakaru matasa majiya ƙarfi domin inganta lamuran tsaro a ɗaukacin faɗin jihar Bauchi.