Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa ta ƙaddamar da shirin rijista layukan sadarwa ga manoma a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

A wani mataki na sauƙaƙa hulɗa tsakanin mambobinta, dama samun damar maki amfana da shirye-shiryen bunƙasa noma, Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa (AFAN) ta ƙaddamar da shirin rijista layukkan sadarwa ga manoma a Sakkwato.

A cewar Shugaban Ƙungiyar Manoman a Sakkwato Jamilu Sunusi Muhammad maƙasudin fitowa da tsarin rijistar layukan CUG ɗin shi ne, sauƙaƙa hulɗar noma daga gab ta farko har zuwa gava ta ƙarshe.

“Kamar su manoma zai sauƙaƙa masu wajen samun bayanai na noma shine gava ta farko, idan an samu bayanan nan, sannan kuma samun iraruwa da taki da kayan da za a sarrafa a yi noman da su a same su a sauƙaƙe, sannan samun dabarun yin noman ma daga malaman noma shi ma a same shi a sauƙaƙe ta wannan layin, sannan sayar da amfanin noma shi ma a yi shi a sauƙaƙe ta hanyar wannan layin da kuma ajiyar kayan gona shi ma duka a wannan layin an fitar da manhaja wacce za ta sauƙaƙa waɗannan abubuwan da muka ambata,” inji Jamilu.

A game da amfanin shirin shugaban ya bayyana cewa tsarin zai rage musu kashe kuɗi wurin yin waya, wanda a cewarsa a yanzu akwai manoman da in ya sa Naira 500 gobe da safe sai ya sa wata ɗari biyar kati, to amma yanzu da wannan tsarin da manoma idan muka samar musu wannan tsarin to duk wanda ya sanya ɗari biyar ƙarshen wannan watan to ba zai sake sa kati ba sai bayan kwana talatin, inji shugaban.

“Don haka idan duka manoman mu suna da shi kowa zai iya kiran kowa da shi, idan ma su sayar da taki na da shi, malaman gona na da shi, duk wanda ke da alaƙa da ƙungiyar noma kuma ya ke da haɗaka da wannan to idan kowa na da shi wannan haɗaka kowa an sauƙaƙa mishi waya kyauta a wata ka ga gajiya ta farko kenan.

Gajiya ta biyu akwai bankin Starling Bank ya shigo da shi aka yi yarjejeniya, za a yi amfani da manhajar wannan tsarin na mu ya riƙa bai wa manoma bashi a sauƙaƙe, wanda duk wanda ya karɓi bashi ba za a sake ba shi wani ba sai ya mayar da wannan, ka ga saɓanin manomi sai ya je ya cike fom, sai ya je ya yi amfani da ka za.”

Ko bayan sauqaqa hulɗa a tsakanin manoma ana sa ran tsarin layin ya tallafa wa manoma wajen samun bashin da zai bunƙasa noman nasu a cewar, a cewar Jamilu Sanusi Muhammad.

Uwar ƙungiyar manoma ta ƙasa dai ce ta fito da shirin wanda aka ƙaddamar da shi a Sakkwato, bisa abinda shugaban na ƙasa ya bayyana a lokacin ƙaddamar da shirin da kyakkyawan tsarin jagorancin ƙungiyar na jihar Sakkwato ke da shi.

Abin da ya sanya ni ma tambayar shugaban na jihar Sakkwato kan ko waɗanne hanyoyi ne suke bi ta yadda za su ilmantar da su yadda za su yi amfani da layin, ko kuma wannan ma tsarin kowa zai iya amfani da shi, shugaban ya kada baki yana mai cewa:

“To kasan in ka cire gwamnati ba ƙungiyar da ta kafu da kyau irin ƙungiyar manoman Nijeriya. Saboda ko wace ƙaramar hukumar mulki muna da mutane guda goma sha tara aƙalla, sannan ko wace mazaɓa muna da exco na mutum tara, waɗanda za su riƙa shiga suna yaɗa bayanai da mun ɗauko bayani cikin ƙanƙanin lokaci ya kai ga manomi na gaskiya, don haka ko ta tsarin wannan mu faɗakar da qananan hukumomi su faɗakar da na mazaɓu su kuma su faɗakar da manoma ko wannan ɗai.

“Sannan duk wasu kafafen watsa labarai da ka sani a jihar Sakkwato ba wadda ba mu ziyarta ba mu ka yi bayani a cikin shiraruwansu masu farin jini, inda manoma na karkara ke saurare mun kai, to kuma muna da hanya ta karɓo bayani, bayan bayani ya isa muna da hanya ta nemo gamsuwar bayanin wato feedback maganizing, wato hanyoyin da za mu iya gane shin labarin nan ya kai ga manoma ko bai kai ba.

“To Alhamdulillahi waɗannan hanyoyin na nuna mna manoma sun karɓi wannan bayanan, tunda yanzu haka ƙananan hukumomi na nan na rijistar layi, kullum muna sanin ko wace ƙaramar hukumar mulki mutum nawa ya karɓa , ko wace mazaɓa mun san ko mutum nawa ya karɓa maza da mata.”

Tuni dai ƙungiyar ta soma rijista ga manoman ƙananan hukumomin Sakkwato ta Arewa da ta Kudu, da Wamakko da Bodinga da Dange Shuni, Tambuwal dama Gwadabawa.