Bashi ya sa kotu ta garƙame shalkwatar First Bank a Abuja

Daga AMINA YUSUF ALI

Babban Kotun Tarayyar ta Abuja ta ba da umarnin garƙame shalkwatar Bankin First Bank a kan bashi. Bankin ya kasance babban bankin Kasuwanci a faɗin Nijeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne dai jami’an kotun suka yi dirar mikiya a Shalkwatar bankin domin ƙwace wasu kayayyaki mallakin bankin.

Hakazalika, rahotannin sun ƙara bayyana cewa, bijire wa umarnin kotun ne ya sa jami’an kotun suka fita a Shalkwatar dake Abuja da motocin janwai domin ƙwace wasu kayayyaki mallakin kotun kamar injin janareto da manyan motoci.

A cikin kayan da aka ɗauka har ma da na’urar sanyaya ɗaki abinda ma’aikatan bankin Kasuwanci suka bayyana da cewa, ba ƙaramin abin kunya ba ne.

Kuma hakan ya sanya musu razani a cikin zukatansu.

Wannan umarni na babban Kotun ya biyo bayan shigar da ƙara da mai bin bankin bashi ya yi a kotu.

Abinda Ya sa kotun ɗaukar ƙazamin matakin. Kodayake dai har yanzu ba a san waye yake bin nasu bashin ba, Kuma ba a san nasa ne ainahin kuɗin da ake bin su ba.

Wannan kutsen da kotun ta yi ya sa hannun jarin bankin ya faɗi da kaso -0.45%, a ranar Juma’ar.

Hakan ya sa bankin ya yi asarar Naira biliyan 1.79, wato ƙarfin arzikin bankin ya koma 393.05 billion, daga Naira biliyan N394.8 da yake a da can.