Ƙungiyoyi sun yi ƙorafin an yi wa ƙananan yara 84,000 rijistar zaɓe a Filato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gamayyar ƙungiyoyin farar hula CSOs, guda goma da ke aiki domin tabbatar da sahihin zaɓe a Nijeriya, sun buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, INEC, da ta gaggauta yin bincike kan rijistar masu zaɓe a Jihar Filato.

Ƙungiyar, a wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Laraba, ta ce ta gano sama da ƙananan yara dubu 84 da suka yi wa rijistar zabe a ƙananan hukumomi 17 da ke jihar.

Vanguard ta rawaito cewa ƙungiyoyin lura cewa, INEC, bisa la’akari da sashe na 19 (1) na dokar zaɓe, 2022, ta wallafa rajistar masu zaɓe a ƙananan hukumomi da mazavun siyasa don tantance jama’a a kowace wurin rajista a faɗin Nijeriya.

“A bisa haka ne tawagarmu ta INEC ta yi wa CSOs da Consultative Partners rajista, suka je Jihar Filato wadda ta ƙunshi qananan hukumomi 17 a ranar 23 ga Nuwamba, 2022, domin mu gani, mu lura da kuma gano wa kanmu halin da ake ciki da kuma matakin da ake ciki.

“Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta shirya gudanar da sahihin zaɓe a shekarar 2023.

“Sakamakon ziyarar gani da ido da muka yi ya nuna akwai sama da masu kaɗa ƙuri’a 84,000 a cikin rijistar da aka buga.

“Mun gano cewa rajistar masu kaɗa ƙuri’a tana cike da ɗumbin ƙananan yara, ciki har da waɗanda ba su kai shekara biyar ba.

“Mun kuma gano cewa yin rajista da yawa game da batun Wase, Kanam, Kanke, Jos North da Sharabutu a ƙaramar hukumar Riyom na da matuƙar damuwa.

“Da’awarmu da rashin amincewarmu, bisa ga sashe na 19 (2), (3) & (4) na Dokar Zave ta 2022, gami da bugu na shaida an gabatar da su ga Jami’an Zaɓe, EO, a cikin ƙananan hukumomin da abin ya shafa don ci gaba da isar da su zuwa ga hukumar zaben.

Kwamishinan, REC, don aiki daidai da sashe na 19 (4) na Dokar Zaɓe.

“Muna kira ga INEC da ta tsaftace rajistar masu kaɗa ƙuri’a a Filato da Nijeriya baki ɗaya,” ƙungiyar ta bayyana a cikin sanarwar da ta fitar ɗauke da sa hannun shugaban cibiyar jagoranci ta Intercontinental, Prince Stafford Bisong.