An cafke matar da ta jefa jaririnta cikin masai a Jigawa

Daga ABUBAKAR M TAHEER

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Jigawa ta sanar da kama wata mata mai suna Balaraba Shehu bayan Jefa jaririn da ta haifa a masai da niyyar binne shi.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tsurma da ke Ƙaramar Hukumar Kiyawa, Jihar Jigawa, inda aka gano jaririn aka garzaya da shi Asibitin Dutse inda a nan aka tabbatar da mutuwarsa.

Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Shiisu Lawan Adam, shi ne ya sanar da hakan ga manema labarai.

Ya ce, “Mun samu labarin jefar da jariri a masai inda jami’anmu suka garzaya domin bincike da kuma kama matar.

“Haka nan, mun kama wani mutum mai suna Amadu Sale wanda ake zargi da yi wa Balaraba ciki tare da ba ta umarnin ta binne yaron da ta haifa inda ita kuwa ta jefa shi a masai,” in ji jami’in.

Tuni dai waɗanda ake zargi suke ci gaba da zama a hannun ‘yan sanda inda a ƙarshe za a tura su kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *