Bashir Baba: Mutuwa rigar kowa

Daga ADAMU NASIRU EL-HIKAYA

Ban gama ajiye alƙalamin ta’aziyyar rasuwar ɗan jarida Muhammad Isa ba da ya zo bayan rasuwar Danladi Ndayebo, sai ga labarin rasuwar Malam Bashir Baba. Duk waɗannan mutanen ’yan jarida ne da su ka yi aiki tuƙuru kuma ba lalle sun tara abun duniya ba. Mutuwa babban darasi ne kuma tunatarwa cewa duk mai numfashi a cikin talikkai to lalle kuwa wataran sai ya ɗanɗani ɗacin mutuwa.

Iyaye ne ko kakanni, dattawa ne ko matasa, maza ne ko mata duk kowa lokaci ya ke jira in kuma lokacin ya yi ba makawa sai tafiya. Na ma tuna marigayi Malam Abubakar Imam a littafinsa MAGANA JARI CE ya radawa wani labari suna “IN AJALI YA YI KIRA KO BA CIWO A JE” don kuwa wani zai shiga sai dai a wayi a ji cewa ai rai ya yi halinsa. Dama ina ji a na cewa rai baƙon duniya don an san shi baƙo dama ya na kan hanya ce da in ka ga a na yi ma sa maraba da zuwa wataran kuma za ka ji a na yi ma sa bankwana.

Hakan faɗakarwa ce cewa ɗaya bayan ɗaya ko biyu bayan biyu ko ma a taron jama’a haka za a yi ta komawa don jiran ranar babban sakamako. Haƙiƙa in an lura za a fahimci cewa kullum sai wani ya rasu amma ba lalle a kan samu labarin rasuwar kowa ba ne.

Ku na gari ɗaya ma ko unguwa ɗaya ma wani zai rasu amma ba mamaki ba za ka ji labari ba ko don irin matakin matsayin sa a al’umma ko rashin ficensa. Wani lokacin ma sai mai lura zai tambaya shin ina wane kaza ne da kan zauna a nan? sai a ba shi amsa da cewa ai rai ya yi halinsa.

Kwanan nan na ziyarci Gombe inda na je kasuwar da a ke cewa LILO don a shekarun da mu ke yara akwai abun lilon yara a kasuwar shi ya sa ta samu sunan ta daga nan. Na shiga kasuwar don cefane inda sai na fara tambayar wani bawan Allah da ya shahara ainun wajen sayar da kayan miya mai suna Malam Musa nan aka ce min ya rasu, na sake tambaya shin ina Muhammad Shushaina wanda mu kan kawo ma sa gyaran takalma, nan ma a ka ce min ya rasu ba da jimawa ba. Ba a ma maganar irinsu Tsoho mai nama da Zannan Gombe da ya ke zama a wata majalisa daf da kasuwar. Haka dai lamarin ya ke dukkan mu lokaci mu ke jira.

Marigayi Malam Bashir Baba dai wanda tsohon ɗan jarida ne da kan yi sharhi kan lamuran yau da kullum a dukkan manyan gidajen rediyon duniya, ya kamu da wata jinya da na samu labarin sai an yi ma sa aiki a samu sauƙin lamarin.

Kasancewar mutumin mu ne mai sauƙin kai wanda kan sada zumunci ya sa jin labarin rashin lafiyar sa da cewa an ba shi gado a babban asibitin tarayya da ke Abuja na kama hanya don duba shi. Haka kuwa a ka yi na shiga ɗakin da ya ke kwance tare da wasu majinyata kimanin 3. Tare mu ka shiga da ɗan jarida Uwais Abubakar Idris.

Na tarar marigayi Bashir Baba na kwance ga tiyon robar ƙarin jini a hannun sa, ga robon tarar bawali a gefensa, ga roba da a ka zura cikin hancinsa don jawo wani ruwa da ya taru a cikinsa! Ya na ganin mu duk da halin da ya ke ciki sai ya yi murmushi don dama da haka a ka san shi.

Ya ɗaure ya miko min hannu mu ka yi musabaha. A nan jiki na ya ƙara ƙarfi don tunanin marigayin na samun sauƙi ne. Mu na nan a zagaye da gadon sai Uwais da ɗan marigayin su ka tafi ɓangaren da za su yi maganar samun jinin da za a yi amfani da shi a washegarin ranar wajen yi ma sa aiki.

Na samu kujera na zauna ina jajanta lamarin sai kawai Bashir ya ce “Malam Nasiru” na amsa na taso ina murna da fatan Allah ya karawa bawan Allah sauƙi. Bayan dawowarsu Uwais sai ga Malam Muhammad I. Usman na shirin IDON MIKIYA ya shigo mu ka gaisa ya na murmushi kuma shi ma su ka gaisa da Malam Bashir har ma ya ke cewa marigayin ai ya tava irin wannan ciwon kuma ya samu sauƙi don haka ba komai don an kama hanyar samun sauƙi.

Muhammad I. Usman ya ƙara da cewa shi kan sa a lokacin bai gama murmurewa daga jinyar da ya yi ba a ’yan kwanakin amma babun tada hankali jinya ce kawai za a warware sarai. A gaskiya I. Usman ya iya kalaman ba da kwarin gwiwa kuma haka a ke so a yayin gaida marar lafiya. Haka mu ka zama har tsawon sa’a ɗaya kafin mu yi sallama mu fice daga ɗakin majinyatan.

Washegari kuwa an samu gudanar da aikin da wajajen ƙarfe 7 na dare a ka kammala amma don yanayin halin da marigayin ya ke ciki sai a ka shige da shi ɗakin kulawa na musamman don haka ba kowa za a iya bari ya shiga ya gan shi ba. Duk da haka na samu labarin likitoci sun yi aiki tuƙuru na matakan magance ciwon da ya ke damun marigayin. Bayan ’yan kwanaki an maida marigayi ɗakin majinyata na kowa da kowa inda mutane na ganinsa har ma ya na magana.

A ido na na ga an kawo ma sa wayar sa ya sanya gilashi ya duba ko rubuta wani sako. Wasu masu karanta wannan bayani za su iya ba da shaidar har marigayin ya amsa mu su wasu daga saƙonnin gaisuwar da su ka aika ma sa alhali ya na gadon jinya. An sake myar da marigayin ɗakin tiyata inda a ka yi ma sa aiki na biyu da hakan ya ƙara sanya shi samun sauƙi.

Allahu Akbar hakanan marigayin ya kasance kwanaki a asibitin ’yan uwa da abokan arziki na zuwa duba shi. Kullum a ka gamu za ka ji an tambayi yaya jikin Bashir Baba kuma a gaskiya mutum ɗaya ya fi kowa shiga juyayi a waɗanda mu ke tare da su don yadda ya kan ziyarci marigayin da sanin duk halin da ya ke ciki.

Wannan mutumin kuwa shi ne dai Uwais na rediyon Jamus. Kullum a ka tambaye shi ya kan ce da sauƙi a sanyaye inda ya kan ƙara da mu cigaba da yi wa Bashir addu’a Allah ya ba shi lafiya. Uwais kan yi magana da ɗan marigayin da ke zama a asibitin don jinyar mahaifinsa kuma ya kan yi magana da likitocin da kan duba marigayin.

Haka duk lokacin da mu ka yi waya da Uwais sai na tambaye shi kuma labarin da ya kan ba ni shi ne ainihin gaskiyar lamarin da ke nuna koma dai me za a ce jinya ba lalle mutuwa ba ce. A ranar jumma’ar makwan jiya Uwais ya shaida min cewa jikin Bashir ya yi tsanani don an ɗora shi a kan na’ura mai taimakawa mutum numfashi na taimakawa rayuwa!

A irin wannan yanayi ya nuna majinyaci ya shiga halin da komai zai iya faruwa don hatta masu jinya a kan ba su shawararsu duƙufa ga yi wa majinyaci addu’a. Ta kan yiwu a lokacin a ce sassan jikin mutum sun dakatar da aiki kama daga ƙoda, hanta da sauransu.

Haka mu ka wuni a ranar jiki a sanyaye inda zuwa sa’o’i goma sha haka zuwa can dare ko a ce sanyin safiyar ranar Laraba Allah ya yi wa marigayi Malam Bashir Baba rasuwa! Iya rayuwar kenan Allah ya karvi abunSa. Ban samu labarin nan ta ke ba don an bugo waya da safe ban lura ba don na tsaya a gidan mai don ganin ba layi na sayi mai na koma gida sai ga waya cewa Allah ya karvi abunsa kuma har ma an kawo marigayin babban masallacin tarayya na Abuja don yi ma sa wanka.

Lokacin da na ke amsa wayar na ji a na cewa a na buƙatar ƙarin mutane a wajen gudanar da wankan da hakan ya tabbatar min Malam Bashir ya koma ga mahalicci. Na nemi na taho masallacin don na halarci sallar jana’iza sai a ka shaida min cewa wankan kaɗai za a yi a nan don za a tafi da marigayin mahaifarsa Wudil a Jihar Kano don yi ma sa jana’iza. Allah ya jiƙan Bashir Baba mai yawan zumunci da rahama.

Kammalawa;

Sau da dama in na gamu da marigayin ya kan tambaye ni da Turanci don farkar da ni na duƙufa kan aiki ya na mai cewa “what is new in town?” ma’ana mene ne sabon labari a gari?

Nan zan kawo batun da a ke ya yi inda za mu tattauna ya faɗa min abun da ya fahimta da yadda ya kamata a duba labarin don isar da shi cikin adalci. Da wannan na ke tunatar da mu cewa wataran sai labari don haka mu yi amfani da duk minti ɗaya na rayuwarmu wajen shuka alheri.