Ɓatagari sun sake ƙona ofishin INEC a Imo

*Sau bakwai ana kai wa ofishin INEC hari a cikin wata huɗi – Kwamishina

Daga WAKILINMU

Ɓatagari sun sake ƙona wani ofishin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ke yankin Ƙaramar Hukumar Oru ta Yamma a Jihar Imo.

Bayanin faruwar hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta fitar ranar Lahadi ta hannun kwamishinanta, Festus Okoye.

A cewar Okoye, Kwamishinan INEC na Jihar Imo, Farfesa Sylvia Uchenna Agu, ya kai rahoton harin da aka kai ofishin da misalin ƙarfe 4.00 asuba ran Lahadi.

Ya ce, ɓarnar da ta auku sakamakon harin ta taƙaita ne a zauren taron ofishin haɗi da kujeru, amma ba ta shafi muhimman kayayyaki ba.

“Baki ɗaya, wannan shi ne karo na bakwai na hare-haren da aka kai a ofisoshin INEC a tsakanin jihohi biyar a cikin wata huɗu,” in ji shi.

Jami’in ya jaddada damuwar INEC kan hare-haren da ake kai wa cibiyoyinta da kuma abin da hakan ka iya haifarwa.