‘Yan bindiga sun harbi liman, sun sace mutum da dama a masallacin Katsina

Daga WAKILINMU

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta ce, ta ceto wasu mutum shida waɗanda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su ranar Asabar a yankin Karamar Hukumar Funtua a jihar.

Ta ce waɗanda aka ceton suna daga cikin mutum 19 da aka yi garkuwa da su a lokacin da suke tsaka da sallar Issha a Masallcin ƙauyen Maigamji.

Bayanan da Manhaja ta samu sun ce, kafin yin awon gaba da waɗanda suka kwashe sai da ɓarayin suka ji wa limamin masallacin da wani mutum guda rauni da harbin bindiga.

Binciken Manhaja ya gano an sako biyu daga cikin waɗanda aka kaɓutar ɗin ne ranar Asabar da daddare, huɗun kuma da safiyar Lahadi.

Da yake tabbatar da aukuwar harin, mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Gambo Isah, ya ce, “Gaskiya ce an kai hari. ‘Yan ta’addan sun kai harin ne a Masallaci a lokacin da jama’a ke gabatar da sallar Issha.

“Inda suka yi harbi da bindiga tare da ji wa limamin da ke jan sallar da wani mutum guda rauni. Yanzu haka ana ci gaba da yi musu magani a asibiti.

“Yanzu saura mutum 13 a hannun ‘yan bindigar, kuma jami’anmu na bakin ƙoƙarinsu don ganin sun ceto su ba tare da sun ji wani rauni ba,” in ji shi.