Ɗan uwan ɗan sanda ya kashe shi ya sace bindigarsa

Wani ɗan uwan wani ɗan sanda ya harbe shi har lahira sannan ya tsare da bindigarsa ta aiki.

Ɗan sandan da ke gadin wani banki ya gamu da ajalinsa a hannun ɗan uwan nasa ne a yayin da suke shirin cin abincin rana a harabar bankin da ɗan sandan yake gadi.

Majiyarmu ta ce, “abin ya faru da ɗan sandan mai muƙamin kofur ne a ranar Laraba lokacin da ɗan sandan ke wanke cokulan da za su ci abinci, bayan ya bar bindigarsa a bisa benci.

“Sai makashin nasa ya ɗauki bindigar ya matsa kunamar sosai inda ya ɗirka masa harbi.

“An kai shi Cibiyar Lafiya ta Gwamantin Tarayya, amma daga baya ya ce ‘ga garinku nan’.”

Majiyarmu ta ce, a makon jiya ne ɗan sandan ya gabatar da makashin nasa a matsayin ɗan uwansa ga jami’an bankin da ke Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.

Majiyar ta ƙara da cewa, wanda ake zargin ya riƙa zama tare da ɗan sandan a harabar bankin kafin ya yi wannan aika-aikar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da afkuwar lamarin.