Rashe-rashen da aka yi a masana’antun finafinan Nijeriya cikin 2022 (1)

Daga AISHA ASAS

Masu karatu barkanmu da haɗuwar farko a sabuwar shekara cikin wannan shafi na Nishaɗi. Barka da ganin sabuwar shekara. Muna taya masoyan Manhaja murnar ganin shekarar 2023, Allah Ya linka mana alkhairan da muka samu a baya, Ya zaunar da mu lafiya a ƙasarmu, Ya azurta mu, Ya bamu cikar burikanmu.

Masu iya magana dai na cewa, waiwaye adon tafiya. Wannan ne ya sa muka yi sha’awar waiwayawa shekarar da muka take, don share fage wurin kawo maku ƙayatattun labarai da tattaunawa tsakanin Manhaja da masu ruwa da tsaki a harkar finafinai har ma da su kansu jaruman.

A kowacce shekara da zata zo ta wuce, takan zo da ababe masu tarin yawa, wasu na daɗi, wasu kuma akasin haka. A cikin ababen da shekara ke zuwa da su sun kasu kasha biyu, akwai sanannu, waɗanda suka zama al’ada a rayuwa, kamar ciwo, rashi da dai sauransu, sai kuma waɗanda ke zuwan ba za ta, irin su vular wata sabuwar anoba da sauransu.

Mutuwa na ɗaya daga cikin sanannun ababen da ke wakana a kowanne lokaci, duk da cewa, ba abu ne da rai ke so ba, sai dai ta zama abokiyar rayuwa da lokaci, wadda duk wani mai rayuwa a ƙarƙashin lokaci ya san da zamanta, kuma ya san zai iya zama ɗaya daga cikin waɗanda ba za a kai ƙarshen shekara da suba, ko ba za a fara sabuwar shekara da suba.

Wannan ne ya sa muka zavi yin waiwaye da waɗanda aka ƙaddara ba za a ga wannan sabuwar shakara da su na daga jarumai da masu shirya fim da ke masana’antun finafinai da muke da su anan gida Nijeriya.

Kamar yadda aka sani, a Nijeriya sanannun masana’antu da muke da su biyu ne, ɗaya a Kudu, ɗaya kuma a Arewa, wato Kannywood da kuma Nollywood. Don haka za mu fara da wasu daga cikin manya-manyan rashe-rashen da aka yi a masana’antar fim ta Arewa, wato Kannywood.

Jarumi Umar Yahaya Malumfashi:

Marigayi Umar

Ɗaya daga cikin sanannu kuma daɗaɗɗu a masana’antar Kannywood, Umar Yahaya Malumfashi ya rasu a ranar Talata, 27 ga watan Satumba, 2022, bayan doguwar jinya da ya yi. Ya rasu ne a wata asibiti da ke Jihar Kano mai suna Pinnacle Special Hospital, kamar yadda Mujallar Fim ta ruwaito. Jarumin ya yi fice a masana’antar, kuma ya kasance ɗaya daga cikin dattijan da suka yi dogon zamani a masana’antar.

Ko a baya-bayan nan, marigayin na ɗaya daga cikin jaruman da suka taka rawa a shahararren shirin nan mai dogon zango na ‘Daɗin Kowa’ wanda tashar Arewa24 ke haskawa.

Baya ga haka, jarumin Umar ya kasance uba da Kannywood ke alfahari da su, kasancewar sa ɗaya daga cikin waxanda suka fara harkar fim tun kan kafuwar masana’antar ta Kannywood. Da yawa daga cikin masu harkar fim da kuma masu kallon finafinan Jarumin sun bayyana matuƙar alhininsu kan babban rashin jarumin mai nagarta, Umar Yahaya Malumfashi, wanda aka fi sani da Bankaura.

Darakta Nura Mustapha Waye:

Marigayi Nura

Mutuwar Darakta Nura Mustapha Waye na layin farko a rashe-rashen da suka girgiza masana’antar fim ta Kannywood, ko kuma ince duk wani ma’abuci finafinan Hausa, kasancewar ya rasu a daidai lokacin da fim ɗin da yake bayar da umurni ke tsaka da samun karɓuwa, wato ‘Izzar So’. Nura Mustapha Waye, ya rasu a ranar Lahadi, 3 ga watan Yuli, 2022, a gidansa da ke unguwar Goron Dutse ta JIhar Kano.

Jarumi Malam Sa’idu Ado Gano:

Jarumin barkwanci Malam Sa’idu Ado Gano, wanda aka fi sani da Bawo, ya rasu a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba, 2022, a gidansa da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Jihar Kano.

Baya ga waɗannan jarumai, an samu rashe-rashe na iyalai da ‘yan’uwan wasu daga cikin jarumai da kuma masu ruwa da tsaki a masana’antar ta Kannywood, kamar rasuwar mahaifiyar fitaccen jarumi Tijjani Faraga, wadda ta rasu a ranar Juma’a, 14 ga watan Oktoba, 2022. Jarumin Mukhtar Hassan SS ya yi rashin mahaifinsa a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu, 2022.

Marigayi Malam Sa’idu

Jaruman nan huɗu da suka fito gida ɗaya, wato Yusuf M. Gidaje, Sabi’u M. Gidaje, Haruna M. Gidaje da kuma Nafi’u M. gidaje, sun yi rashin mahaifinsu a rana ɗaya da rasuwar mahaifin abokin aikinsu, Mukhtar Hassan, wato 4 ga watan Afrilu. Jarumi Balarabe Jaji, a ranar Asabar, 26 ga watan Maris, 2022, ya yi babban rashi, inda ‘ya’yansa huɗu, mata uku, namij ɗaya, suka rigamu gidan gaskiya ta sanadiyyar haɗarin mota.

Shi ma mawaƙi Yusha’u Ahmad, wanda aka fi sani da Ishe Baba, ya yi rashin mahaifiyarsa a wannan shekara da ta gabata. Mawaƙi Abdul Tynkin ma ya shiga jerin waɗanda suka yi babban rashi a shekarar 2022, inda ya rasa mahaifiyarsa a ranar Lahadi, 4 ga watan Satumba, 2022, a garin Lafiya, Jihar Nassarawa. Allah Ya ɗauki ran ɗan mawaƙi Abubakar Yarima a ranar Lahadi, 10 ga watan Afrilu, 2022.

Furodusa Magaji Sulaiman ya yi rashin ɗansa a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba, 2022. Shi kuwa Furodusa Magaji Sulaiman ya rasa matarsa a ranar Litinin, 22 ga watan Agusta, 2022, a Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya, wato ABUTH.

Ta vangaren Furodusa Salisu Umar Salinga, an jarrabece shi da rashin ‘yarsa a ranar Alhamis, 28 ga watan Yuli, 2022 a gidansa da ke Jihar Kaduna. Shi kuwa Furodusa Magaji Sulaiman ya yi rashin matarsa da kuma ɗansa duk a wannan shekarar ta 2022.

Tsohon shugaban Ƙungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, Malam Murtala Muhammad Aniya, ya yi rashin ‘yarsa Fatieha a ranar Lahadi, 26 ga watan Yuni, 2022, a asibitin da ke Tudun Nufawa, Jihar Kaduna.