Mu’assasin AMAA, Peace Anyiam-Osigwe ta rasu

Daga WAKILINMU

Gwarzuwar shirya fina-finai a Nijeriya kuma mu’assasin Cibiyar ba da Kyaututtuka Kan Shirya Fina-finan Afirka (AMAA), Peace Anyiam-Osigwe, ta kwanta dama.

Fitaccen darakta, Obi Emelonye ne ya tabbatar da rasuwar tata a shafinsa na Instagram da safiyar Talata.

An ga yadda ya wallafa hotonta haɗi da saƙon ban-bakwana a shafin nasa.

Kafin rasuwarta, marigayiyar ita ce Shugabar ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ‘Association of Movie Producer.’

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *