An cafke ‘yan bangar siyasa 50 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jami’an kwamitin yaƙi da ‘yan dabar siyasa a Jihar Zamfara sun kama wasu ‘yan bangar siyasa magoya bayan Kam’iyyar PDP aƙalla mutum 50 a garin Gusau, babban birnin jihar.

Shugaban kwamitin, Bello Mohammed Bakyasuwa ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a ofishinsa ga manema labarai ranar Talata.

Bello ya ce, sama da mutum 30 daga cikinsu an same su da muggan makamai yayin gangamin siyasar ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Dr. Dauda Lawal Dare a Gusau.

Ya ƙara da cewa, an kama su ne a lokacin da suke ƙoƙarin tada tarzoma tare da yunƙurin lalata kayyayyakin gwamnati da na Jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

Bakyasuwa ya bayyana cewa kwamitinsa ya kama wani Yusuf Aminu Gusau da ake zargin PDP ce ta ɗauki nauyinsa yayin da ya cinna wa wata motar APC wuta a Gusau kwana ɗaya bayan ɗan takarar gwamnan Jamiyyar PDP, Dr. Dauda Lawal Dare ya shigo Gusau.

A wata hira da manema labarai, Yusuf Aminu Gusau ya amsa cewa ya cinna wa motar APC wuta .

A cewarsa, ya yi aiki ne da umarnin da ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Dakta Dauda Lawal Dare ya bayar na cewa su ƙona duk wata motar APC a lokacin gangamin siyasar da ya yi ranar Litinin a Gusau.

“Na yi abin da na yi ne bisa umarnin da aka ba mu ta hannun shugabanmu cewa, Dokta Dauda Lawal Dare ya ce mu yi gaba a yayin taron nasa, tare da tabbatar da duk motar APC da muka samu ta tare babbar hanyar shiga Gusau mu kawar da ita da ƙarfin tsiya, ko kuma a ƙona ta baki ɗaya,” in ji Yusuf Aminu.

Bakyasuwa ya bayyana cewa kwamitinsa zai yi aiki tukuru domin ganin an rage duk wani nau’in ‘yan dabar siyasa, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ko aikata laifuka a jihar musamman a lokutan yaƙin neman zaɓe, da Kuma lokacin gudanar da zaɓe mai zuwa don tabbatar da samun ingantaccen tsaro da zaman lafiya a faɗin Zamfara.

Ya ce nan ba da jimawa ba kwamitin zai miƙa dukkan masu laifin ga ‘yan sanda domin ci gaba da ɗaukar mataki da ya dace a kansu.