‘Yan sandan sun cafke ‘yan bindiga 2, sun ƙwace tarin alburusai a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama wasu da ake zargin masu yi ‘yan bindiga safarar makamai ne a jihar.

Kakakin rundunar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau ranar Talata.

A cewarsa, abubuwan da aka ƙwato daga wajensu sun haɗa da harsashi guda 325 da kuma bindigar Ak47 guda ɗaya.

“A ranar 8 ga Janairu, 2023 ne jami’an ‘yan sanda suka kama wasu ‘yan bindiga biyu, Emmanuel Emmanuel da takwararsa Nana Ibrahim a kan hanyar Gusau, Wanke zuwa Dansadau, da harsasai 325 da bindigar Ak 47 a yunƙurinsu na kai wa ‘yan ta’adda,” in ji jami’in.

A cewar sanarwar, an kama su ne biyo bayan bayanan sirri da aka samu game da safarar makaman daga Jihar Binuwai zuwa sansanin ‘yan bindiga da ba a bayyana ba a Zamfara.

Ya ƙara da cewa, yayin bincike waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna sana’ar sayar da bindigogi ga ‘yan bindiga da ke jihar ta Zamfara da sauran jihohin da ke makwabtaka da ita.

Rundunar ‘yan sandan ƙarƙashin Kwamishina CP Kolo Yusuf, ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin cafke abokan hulɗarsu tare da gurfanar da su gaban kotu.

“Kwamishanan ‘Yan Sanda, CP Kolo Yusuf ya bada tabbacin ‘yan sandan jihar sun ba da himma da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar, sannan ya buƙaci jama’a da su haɗa kai da jami’an tsaro a wannan fanni,” in ji Sanarwar.