Taimakon jin ƙai a lokacin sanyi

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A lokacin ƙarshen shekara tsakanin watannin Nuwamba da Disamba har zuwa Maris, a kan samu canjin yanayi da ke juyawa zuwa sanyi ke kasancewa da tsanani a wani wajen lokaci zuwa lokaci. A bana dai Hukumar Kula da Yanayin Muhalli ta Ƙasa, Nimet ta bayyana cewa, za a samu yanayin sanyi da hazo mai tsanani a wasu jihohin Arewa wanda ya taso daga yankin hamadar ƙasashen Chadi da Nijar.

A cewar rahoton hazon da ke haɗe da ƙura zai shafi jihohin Borno, Yobe, Gombe, Katsina, Kano, Kaduna, da Jigawa za su samu hazo sosai, yayin da yankin Arewa ta Tsakiya za su samu matsakaicin hazo. Sannan lokaci ne da ake danganta shi da wasu nau’in cututtuka da suka haɗa da cutar mura, tari, asma, da sanƙarau. Don haka ake shawartar jama’a da su riqa kulawa da irin suturar da suke sanyawa a yayin da za su fita waje,domin kare lafiyarsu, musamman ma kuma ƙananan yara, da masu sikila ko ƙan jikin idanu.

A irin wannan yanayi ne ake samun ƙalubalen tashi da saukar jiragen sama, saboda yadda hazo ke rufe sararin samaniya yana hana su gudanar da ayyukan sufuri jigilar jiragen, kamar yadda Hukumar Nimet ta bayyana a farkon rahoton ta.

Wani ɓangare mai muhimmanci da ke fuskantar matsala a lokaci kamar wannan, shi ne wajen kula da lafiyar yara masu yawo a titi ba tare da samun kulawar iyaye ba, kamar almajirai da marayu waɗanda suke rayuwar yawon bara da neman abin da za su ci, cikin tsumma da rashin kulawa, ga rashin wanka, da rashin lafiya. Rayuwar waɗannan yara da shekarun su ke kamawa daga 5 zuwa 13 na kasancewa cikin ƙunci da galabaita, saboda yanayin da ake ciki, da kuma yadda tausayawa da jin ƙai ke wahala a wajen jama’a, waɗanda za su iya taimaka musu a matsayin sa’o’in yaransu.

Hatta wuraren da irin waɗannan yara ke kwana tsangayu ne na karatun allo, da ko kyakkyawan rufi, ko abin shimfiɗa babu. Wasu yaran na kwanciya ne a kan tabarmi ko dandamalin siminti inda sanyi ke kwanciya, a dalilin haka kuwa yara na iya kamuwa da cututtuka masu nasaba da sanyi, kuma ba lallai ne a samu damar saya masa magani ko kai shi asibiti ba. A irin wannan lokaci na sanyi sai almajiri ya yi sati bai yi wanka ba, idan ba malamin sa ya yi masa magana ba, kuma ko ya so yi ɗin ma babu inda zai samu ruwan ɗumi ya gasa jikinsa, haka zai je rafi ko ya watsa ruwan jikinsa na karkarwa, gwanin ban tausayi.

Wani almajiri, Sahabi Nasiru ɗan shekara 7 daga Ƙaramar Hukumar Minjibir a Jihar Kano, ya koka da yanayin wajen da suke kwana. Ya ce, “ba ni da suwaita, na ni da bargo, sai wani ƙaramin zani da mamana ta bani, akwai sanyi sosai in mun zo kwanciya, kuma ga shi babu gidan sauro.”

A irin wannan lokaci ne ake samun ƙungiyoyin sa kai masu gudanar da ayyukan jin ƙai da taimakon al’umma suna gudanar da wasu ayyukan raba suwaitu da kayan sanyi don tausayawa halin da waɗannan yara ke ciki, da nufin samar musu da suturar da za su kare jikinsu daga tsananin sanyin da ake yi, da kuma kare lafiyar su.

Ƙungiya ta baya bayan nan ita ce ƙungiyar Motherhen Initiative, da ake yi wa laƙabi da Kaza Uwar ‘Ya’ya, wacce ta gudanar da wani aikin jin ƙai irin wannan a garin Jos, inda ta rabawa yaran almajirai rigunan kare sanyi, irin su suwaita, takalmi silifas, man shafawa, da garin sabulun wanki da na wanka. Domin yaran su tsaftace jikinsu da kare tsiraicin su.

Shugabar ƙungiyar, Hajiya Larai Binta Hassan ta bayyana cewa, lura da irin yanayin sanyin da ake yi a Jos, da kuma nazari kan halin da yaran almajirai da marasa gata suke ciki, na yiwuwar takura da kamuwa da wasu cututtuka masu nasaba da lokacin sanyi, ya sa ƙungiyar ta tattara ɗan abin da take da shi, ta sayi suwaitu da sauran kayan da suka raba wa yaran, don su taimaka musu wajen rage tsananin sanyin da ake yi a Jos.

Ta koka da yadda yanzu rayuwa ta koma kowa ‘ya’yansa kawai ya sani, bai damu da halin da yaran da ke rayuwa a titi ko almajirai ke ciki ba. Tausayawa waɗannan yaran ne ya sa suka yi tunanin ɓullo da wannan shiri na tallafawa.

Ita ma Hajiya Maryam Baba Bala da ke jagorantar wata ƙungiyar tallafawa mabuƙata da kyautata zamantakewar iyali, ta bayyana cewa, ƙungiyar Women In Leadership Initiative (WiLi Africa) ta tallafawa yaran almajirai da marayu da almajirai fiye 500, da kayan sanyi da suka haɗa da suwaitu, hular sanyi, safar qafa da safar hannu har da bargo.

A cewar Maryam B.B, ɗa ko ba kai ne ka haife shi ba, ya kamata ka tausaya masa ganin halin da yake ciki, domin mutum ba zai bar ɗan cikinsa a wani yanayi marar kyau da zai cutar da rayuwarsa ba. Ta kuma yi kira ga iyayen da ke tura yaransu zuwa makarantun tsangaya don neman haddar Alqur’ani mai girma da su riƙa tunawa da irin wannan yanayi suna aikawa yaran da kayan sanyi da barguna, don taimaka musu, samun sauqin rayuwa a inda suke karatu, domin kuwa yaransu amana ce a wajen su, bai kamata su sarayar da haƙƙoƙin da ke kansu ba, zuwa kan al’umma.

Ko ma ba marayu da almajirai ba, mutum in yana da hali zai iya sayen kayan sanyi ko barguna ya raba wa yaran makwafta da ‘yan gudun Hijira da ke rayuwa cikin wani muwuyacin hali, da ke buqatar taimako, wanda hakan zai iya zama masa kaffara a wajen Ubangiji. Kamar yadda malamai suke karantar da mu cikin hadisai cewa, Allah ya gafartawa wata karuwa sakamakon tausayawa wani kare da ke cikin halin qishir ruwa. Kamar misalin haka ne rayuwar waɗannan yara da ke cikin tsananin buƙatar taimakon gaggawa a wannan yanayi na matsabancin sanyi, musamman da daddare ko da asuba.

Ya kamata a riqa samun ƙungiyoyin da za su riƙa bai wa irin waɗannan yara tallafi, don ceto rayuwarsu da inganta lafiyarsu. Kada ya tsaya ga suwaita da man shafawa da sabulun wanka. A samu wasu kuma da za su sake inganta musu ginin makarantu, wurin kwanan su, har ma da abincin da za su ci, domin ɗauke su daga titi suna yawon bara.

Gwani Jibrin Yahaya Alƙasim, Shugaban Ƙungiyar Inganta Makarantun Tsangaya na Ƙasa, ya yi kira ga hukumomi da su riƙa ɗaukar waɗannan almajirai a matsayinsu su ma na ‘yan ƙasa da ke rayuwar ɗalibta ta neman ilimi. Yayin da yake jinjinawa ƙungiyar Motherhen da sauran ƙungiyoyin da ke tallafawa rayuwar almajirai, Gwani Jibrin ya kuma nemi sauran al’umma da su riƙa kallon waɗannan almajirai kamar ‘ya’yan da suka haifa, tare ba su dukkan tallafi da goyon bayan da suke buƙata, domin gobe ba su san wanda zai taimaki nasu yaran ko su kansu ba.

Dangane da wani labari mai ƙarfafa gwiwa da ya yi kama da irin wannan kira da ake yi, wani abu ya taɓa faruwa a wani gari a wata ƙasa, inda wani ɗalibi da yunwa ta galabaitar yana tafiya yana tangaɗi, ya isa ƙofar wani gida ya yi sallama tare da roƙon a taimaka masa, kada yunwa ta kashe shi. Matar gidan da ta lura da halin da yake ciki ta tausaya masa, sai ta shiga ta fito masa da ƙwaryar madara ta ba shi, ya sha kuzarin jikinsa ya dawo, ya yi mata godiya ya tafi. Bayan wasu shekaru, matar nan ta tsufa, ciwo ya ci ƙarfinta, ga masu gidan da take haya na matsa mata a kan kuɗin haya da ake bin ta. Sai kawai ta ga wasu ma’aikata sun shigo gidan suka miqa mata wata takarda, wacce a tunaninta takardar sallama ce daga gida, sai ta ga takardar mallaka mata gidan ce. Da ta nemi bayani, sai aka miƙa mata wata takarda da a jiki an rubuta, Sakayyar Ƙwaryar Madara!

Wannan ya nuna mata cewa, wancan ɗan makarantar da ta taimakawa da Ƙwaryar Madara shi ne yanzu Allah ya yi wa arziki, bayan kammala makaranta, ya koma domin sakanta mata da aikin alherin da ta yi masa. Bayan saya mata gida da aka yi kuma, ya sa aka kai ta wani babban asibiti shahararre don a duba lafiyarta, a yi mata magani.

Ire iren wannan labari suna nan da dama, da za su zame mana kyakkyawan abin misali cewa, ba duk wanda ka kyautatawa ne yake juyewa ya cutar da kai ba, wani alherin sai ka juya ka manta da shi, sannan taimakon Allah yake zuwa ta inda ba a zata ba! Shi ya sa Bahaushe ke cewa, Alheri danƙon ne ba ya faɗuwa ƙasa banza!!