2023: Adamu ya nemi dafawar Ubangiji kan nasarar Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nemi dafawar Ubangiji don ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyarsu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kai bantensa a babban zaɓe mai zuwa.

Adamu ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci shugabancin jam’iyyar (NWC) zuwa ofishin kamfe ɗin Tinubu/Shettima da ke Abuja a farkon wannan makon.

Sa’ailin da yake jawabi yayin ziyarar, Shugaban APCn ya yaba da tsare-tsare da shirye-shiryen da Tinubu ke yi don gudanar da yaƙin neman zaɓensa.

Adamu ya faɗa wa Tinubu, “Duba da ƙoƙarin da ka yi, hakan wata alama ce mai nuni kana tare da nasara. Waɗanda suka san ka, ba su sa ran ganin ƙasa da haka daga gare ka.

“Kuma muna fata da addu’ar Allah Ya tabbatar mana da nasara a Fabrairun 2023,” inji Adamu.

Tun farko da yake jawabi, Tinubu ya yaba wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan biyayyarsa ga jam’iyya da kuma matsayar da ya yi cewa shi ba zai zaɓi kowane ɗan takara ba sai wanda APC ta tsayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *