William Tubman: Wanda ya zamanartar da Laberiya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Laberiya ƙasa ce ta ‘yantattun bayi, wadda aka gina da musguna wa ‘yan ƙasar lokacin da aka zaɓi William Tubman a matsayin shugaban ƙasa. Bayan haɗa kan mutane, ya shirya ƙasar bisa tsarin ci-gaba wanda bai samu ba.

An haifi William Vacanarat Shadrach Tubman ranar 29 ga watan Nuwamba 1895. Ya fito daga yankin kudu maso gabashin Laberiya, daga garin da ake kira Harper na gundumar Maryland.

Sunan wuraren ya yi kama da na Amurka, saboda Jamhuriyar Laberiya ta ayyana samun ‘yanci daga Amirka a shekarar 1947 da ‘yantattun bayi suka yi, waɗanda suka dawo daga Amirka a lokuta dabam-dabam a tsawon shekaru 50 a farkon ƙarnin.

Mahaifin Tubman yana cikin ‘yantattun bayi 69 da suka tafi Laberiya a shekarar 1944. Mahaifiyarsa ta fito daga Atlanta, Georgia.

Tubman ya girma ƙarƙashin kulawar mahaifinsa mai wanda ya gwada wa ‘ya’yansa tafarkin addini na yin addu’a da hana yaran kwanciya a kan gado saboda kar su shagala.

Tubman, wanda ya kasance shugaban Laberiya na 19, da kuma ya jagoranci ƙasar daga shekarar 1944 zuwa 1971, mutum ne da ake yi wa kirarin baban Laberiya na zamani.

Ta hanyar amfani da dukiyar da masu saka jari suka samar a ƙasar, ya gina hanyoyin mota da na jiragen ƙasa tare ma da inganta matsayin tashar jiragen ruwa da ke Monrovia babban birnin ƙasar. Haka nan ya samar da ingantaccen yanayi na fitar da roba da tama da ƙarafa zuwa ƙasashen duniya.

Bayan mutuwar William Tubman, Laberiya tana da babbar cibiya ta kasuwanci da ta yi suna a duniya. Yawancin muhimman gine-gine irinsu majalisa da zauren taro na Monrovia da cibiyar ɗaukaka al’adu da a yanzu ake kira Kendeja, duk sun samu ne a zamaninsa.

Hakazalika, shi ne ya gina fitaccen katafaren Otel ɗin nan wato Ducor International, ɗaya daga cikin fitattun Otel a yammacin Afirka.

Lokacin mulkin Tubman, Laberiya ta samu bunƙasa. Gwamnatinsa ta kyautata fannonin ilimi da lafiya. Ƙasar ta rungumi tsarin yaƙi da jahilci da ake yi wa laƙabi da “Each one teach one”.

Wani abin kuma shi ne, Tubman ya yi ƙoƙarin daidaita tare da haɗa kan ‘yan Laberiya. ‘Yan ƙasar da ke da ƙarfin faɗa a ji masu alaƙa da Amirka sun muzguna wa ‘yan ƙasar cikin wasu shekaru kusan shekaru 100. Sai dai gwamnatin Tubman ta tabbatar da tsarin bai ɗaya na ‘yanci tsakanin mutane.

Amma, mulkin shekaru 27 na William Tubman bai rasa samun suka daga wasu ɓangarori na ƙasar ba. Yaqin basasar da ya afku a shekarun 1980, abu ne da ya sanya alaƙanta shi da samo asali daga ginshikin da tsohon shugaban ya kafa.

An dai zarge shi da kama-karya da kuma rayuwa ta bushasha. Haka nan alaƙarsa ta ƙut-da-ƙut da Amurka ta sanya wasu cewa ita ta raba ƙasar da ‘yancinta. Domin girmama shi da abubuwan da ya samar, an ware ranar haihuwarsa a matsayin ranar hutu a faɗin ƙasar.

Wasu kalamai fitattu da William Tubman ya yi a baya:

“Laberiya ba ta samu diyyar mulkin mallaka ba. Ba mu ƙaddamar da yaki kan tsarin gurguzu ba, muddin dai bai wuce iyaka ba, amma muna iya yaƙar duk wani yunquri na tilasta mu yin abin da ya wuce hankalinmu”.