2023: Rundunar ‘yan sandan Kano ta gana da sauran hukumomin tsaro

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

A ranar Talatar da ta gabata ne rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Mamman Dauda ta gana da Hukumar Zaɓe reshen Jihar Kano da sauran hukumomin tsaro dake jihar, don ɓullo wa matsalolin da ka iya bijirowa yayin gudanar da zaɓen shekarar 2023.

Da yake jawabinsa lokacin taron, shugaban kwamitin hukumomin tsaro na Jihar Kano kuma jagoran rundunar ‘yan sandan ta Kano CP Mamman ya bayyana cewa wannan taron na da nufin samar da kyakkyawan tsaro a dukkan guraben jefa ƙuri’a kimanin 11,222 dake akwai a faɗin ƙananan hukumomi 44 dake jihar.

CP Mamman Dauda ya kuma buƙaci sauran hukumomin tsaro dake jihar da su gabatar da sunayen dukkan jami’an da za su kasance cikin waɗanda za su kula da ɓangarorin zaɓe kafin ƙarshen wannan shekara.

Haka kuma kwamishinan ‘yan sandan ya kuma buƙaci sauran sashen tsaron da su kasance masu bada haɗin kai wajen ciyar da wannan jiha gaba da ma ƙasa baki ɗaya.

A ɗaman da ya gudana dake ɗauke da hukumomin tsaron da suka haɗa da Civil Defence, Jami’an Hukumar Shigeda Fice, Sojojin Sama, Sojojin Ƙasa, FRSC, Hukumar Zaɓe, ‘yan sanda, jami’an sirri, wanda dama ya zuwa yanzu shirye-shiryen hukumomin tsaron kan batun zave ya yi nisa na bada kariya ga hukumar zaɓe, kayan zaven da kuma guraren da za a gudanar da zaɓen da su kansu ma’aikatan da za su gabatar da zaɓen.

Daga ƙarshe, dukkan jami’an tsaron da suka halarci zaman sun bada ƙarin shawarwari wajen tsare-tsaren, sannan sun ƙara bada tabbacin bayar da goyon baya, don ganin an samu nasarar gudanar da aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *