Mun karɓe Naira biliyan 30 a hannun dakataccen Akanta-Janar, Ahmed Idris – EFCC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa, ta ce, zuwa yanzu an karve Naira Biliyan 30 daga hannun dakataccen Akanta-Janar, Ahmed Idris. 

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa waɗannan biliyoyi su na cikin Naira biliyan 109 da ake zargin Ahmed Idris ya karkatar a lokacin yana riqe da ofishin Akanta Janar na Ƙasa. 

Shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa ya shaida wa duniya wannan a lokacin da ya halarci wani taro da aka yi da manema labarai jiya.

EFCC ba ta yi cikakken bayani a kan kuɗin da aka karɓe a hannun Idris ba. Tuni dai Ministar Tattalin Arziki ta dakatar da shi domin a iya binciken sa. 

Kwamitin Harkokin Yaɗa Labarai na Fadar Shugaban Ƙasa ta shirya wannan zama a Aso Villa a Abuja kamar yadda aka saba lokaci bayan lokaci. 

Kamar yadda Abdulrasheed Bawa ya yi bayani, ya ce hukumar su ta karɓe biliyoyi a shekarar 2022, daga watan Janairu zuwa Disamban 2022, sun karɓe Naira 134,33,759,574.25, $121,769,076.30, da £21,020.00. 

A tsakanin wannan lokaci, hukumar ta yi nasarar karɓe €156,925.00, ¥21,350.00, da CFA300,000.00. 

Bawa ya ce sun ɗaure mutane fiye da 3,615 a shekarar nan, wanda hakan ya nuna da gaske ake yi wajen yaƙar masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati. 

Punch ta ce a jawabin da ya yi, Bawa ya shaida cewa za a bi doka da ƙa’ida wajen yin gwanjon wasu motoci da aka karɓe daga hannun marasa gaskiya. 

Bayan an yi gwanjon waɗannan abubuwan hawa, akwai gidajen 150 da EFCC za ta sa a kasuwa, za a saida su ga mutanen da suka nuna sha’awar saye. 

Wani albishir da shugaban na EFCC ya yi shi ne, da zarar sashen SCMUL ya fara aiki gadan-gadan, zai yi wahala wani mutum ya iya satar kuɗi a Nijeriya. 

SCMUL wani sashe ne na musamman da aka ƙirƙiro da nufin yaƙar masu satar kuɗi ta haramtaciyyar hanya. An fito da wannan tsari a shekarar 2011.