Gwamna Masari ya sallami Mataimakin Shugaban Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua

Daga UMAR GARBA a Katsina

Majalisar Zartaswar Jihar Katsina ƙarƙashin jagoracin Gwamna Aminu Bello Masari ta umarci Shugaban Jami’ar jihar Farfesa Sanusi Mamman da shugaban hukumar gudanarwa na jami’ar da su ajiye muƙamansu ba tare da ɓata lokaci ba.

Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan ilimi mai zurfi Dakta Bashir Usman ruwan godiya ne ya bayyana haka a ƙarshen zaman majalisar da ya gudana ranar Laraba a Fadar Gwamnatin Jihar.

Sauke shi daga muƙamin ya biyo bayan rahoton da kwamitin da Gwamna Masari ya kafa a kan ya ba shi shawara dangane da ƙorafe-ƙorafen da aka yi wa shugaban jami’ar kamar yadda rahotanni suka nuna.

Ruwan goɗiya ya bayyana cewar kwamitin da aka naɗa ya gano cewar shugaban jami’ar ya aikata ba daidai ba gami da sava dokokin da suka kafa jami’ar, harkar kuɗi da kuma sha’anin mulki.

Mai bai wa gwamnan shawara ya kuma bayyana cewar kwamitin ya bada shawarar cewar barin shugaban jami’ar ya ci gaba da kasancewa kan muƙaminsa zai iya kawo naƙasu ga cigaban jami’ar.

Daga nan sai ya bayyana cewar majalisar zartarwar ta amince da sake yin nazari dangane da dokokin da suka kafa jami’ar domin samun ƙarin cigaba a harkokin koyo da koyarwa. 

Ya kuma ce bada jimawa majalisar zartaswar za ta amince da naɗin waɗanda za su cigaba da tafiyar da jami’ar a matsayin shugaba da kuma shugaban gudanarwa.