Buhari ya maƙala wa Yahaya sabon muƙaminsa

Spread the love

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya maƙala wa Shugaban Rundunar Sojoji (COAS), Lt Gen Faruk Yahaya, sabon muƙaminsa a matsayin Lieutenant General.

Buhari ya aiwatar da hakan ne tare da taimakon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo wanda ya gudana jim kaɗan kafin soma taron Majalisar Zartarwa na wannan makon da ya gudana a Larabar da ta gabata a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala maƙala masa sabon muƙamin nasa, Yahaya ya yaba wa Shugaban Ƙasa bisa damar da ya ba shi don yi wa ƙasa aiki da kuma jagorancin rundunar sojoji a matsayin shugaban rundunar na 22.

Daga nan, Yahaya ya yi alƙawarin gudanar da ayyukansa cikin ƙwarewa da kuma kamanta gaskiya.

Kazalika, ya bayyana wa Shugaban Ƙasa tabbacin zai kasance mai biyayya ga Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya.

Waɗanda suka shaida bikin sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Ministan Tsaro, Major General Bashir Salihi Magashi da Shugaban Tsaro, General Lucky Irabor da Matar Faruk Yahaya, Salamatu Faruk Yahaya da dai sauran manyan jami’an gwamnati.

By Editor